An kori shugabannin yanki a Edo

Majalisar Jihar Edo ta kori Sshugabannin kananan hukumomi biyu daga bakin aiki a jihar a sakamakon binciken da kwamitin da majalisar jihar ta kafa dangane da zargin da aka yi masu na rashin iya gudanar da aiki ga jama’a da suka nuna a fili.Shugabannin su ne  na karamar Hukumar Oredo, Osaro Obazee da Mista Emmanuel […]

An kori shugabannin yanki a Edo
An kori shugabannin yanki a Edo

Majalisar Jihar Edo ta kori Sshugabannin kananan hukumomi biyu daga bakin aiki a jihar a sakamakon binciken da kwamitin da majalisar jihar ta kafa dangane da zargin da aka yi masu na rashin iya gudanar da aiki ga jama’a da suka nuna a fili.
Shugabannin su ne  na karamar Hukumar Oredo, Osaro Obazee da Mista Emmanuel Momoh na karamar Hukumar Etsako Central kuma wannan korar da aka yi musu kamar yadda majalisar jihar ta nuna, ta yi haka ne domin tsabtace ayyukan gwamnati a jihar. Bayanin ya ci gaba da cewa, bincike ya tabbatar da cewa shugabannin da aka sallama daga aiki, ba su bin ka’idar aikin gwamnati. An ce dukkansu biyun ba su biyan ma’aikatansu  hakkokinsu na aiki a kan lokaci.
Kamar yadda binciken Aminiya ta gano, tun a ranar 6 ga watan Oktoba n bara ne aka fara tuhumar shugabannin kananan hukumomi guda hudu a cikin jihar amma sai kwamitin binciken ya zartar da sallamar guda biyu, bisa kwararan hujjojjin cewa ba su tafiyar da aikin gwamnati bisa ka’ida, kamar kuma yadda aka gano cewa suna yin wasa da aiki.
Su kuma sauran guda biyun, Mista bictor Enobakhare Roland da Mista Ibieoru Touwan na kananan hukumomin Orhionmwon da Egor da suka rage, wadanda suke a kan siradi, an bayyana dalilin daga musu kafa da kwamitin ya yi, inda aka kasa samun kwararan hujjojin da za a dogara da su, dangane da tuhumar da aka yi musu.