An kori Tijjani Babangida daga Eagles

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayar da sanarwar korar Tijjani Babangida a matsayin mai taimaka wa koci Sunday Oliseh na musamman a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.Sai dai hukumar ba ta bayyana takamaiman dalilin da ya sa ta kori Tijjani Babangida daga kan mukamin nasa ba.Amma wata majiya ta tabbatar […]

An kori Tijjani Babangida daga Eagles
An kori Tijjani Babangida daga Eagles

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bayar da sanarwar korar Tijjani Babangida a matsayin mai taimaka wa koci Sunday Oliseh na musamman a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles.
Sai dai hukumar ba ta bayyana takamaiman dalilin da ya sa ta kori Tijjani Babangida daga kan mukamin nasa ba.
Amma wata majiya ta tabbatar cewa an kore shi ne saboda amincewa da kalaman da koci Sunday Oliseh ya yi ne a kwanakin baya, inda ya caccaki NFF a bisa gazawarta na kula da ’yan kwallon Eagles a gasar cin kofin matasa na Afirka (CHAN) da ya gudana a Ruwanda, da hakan ta sa aka cire kungiyar a gasar tun a zagayen farko.
Bayan an fitar da Najeriya ne sai aka ji kocin yana babatu a kafofin yada labarai ciki har da na shafukan zumunta na facebook da twitter da sauransu inda ya nuna kada a zargi kowa sai NFF saboda irin rikon sakainar kashin da ta yi wa kungiyar Super Eagles a lokacin gasar.
Wadannan kalamai da kocin ya yi sun yi matukar bata wa NFF rai al’amarain da ya sa ta kafa kwamitin ladabtarwa don binciken kalaman da kocin ya yi.
A rahoton da kwamitin ya gabatarwa NFF ne ya bayar da shawarar a kori Tijjani Babangida, yayin da shi kuma koci Sunday Oliseh aka aika masa da takardar gargadi ta karshe (last warning).
Rahotanni sun nuna Sunday Oliseh ya aika da takardar neman afuwa ga kwamitin ladabtarwar a kan kalaman da ya yi al’amarin da ya sa ake ganin kwamitin ya sassauta masa inda ya dauki matakin aika masa da takardar gargadi ta karshe maimakon ta kora.
Haka nan rahoton bai ambaci ko za a maye gurbin Babangida da wani sabon jami’i ba ko a’a.
Kwamitin ya umarci Oliseh da cewa daga yanzu tilas ne ya rika tuntubar hukumar NFF a duk al’amurran da suka shafi kungiyar Super Eagles musamman wajen zakulo ’yan wasa da yin tafiye-tafiye da sauransu kafin a amince masa.
An zabi Tijjani Babangida a matsayin mataimaki na musamma ne a kungiyar Super Eagles jim kadan bayan an nada Sunday Oliseh a matsayin kocin kungiyar a bara.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa