An kori wani dan sanda kan laifin fyade
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta tube kakin wani jami’inta bisa kama shi da laifin fyade dumu-dumu. Makonni biyu da suka gabata ne aka kama dan sandan mai suna Kofur Sani Salisu Gwagwarwa sakamkon yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara bakwai da fyade a Unguwar Gwagwarwa da ke birnin Kano.Kakakin Rundunar ASP Magaji Musa […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta tube kakin wani jami’inta bisa kama shi da laifin fyade dumu-dumu.
Makonni biyu da suka gabata ne aka kama dan sandan mai suna Kofur Sani Salisu Gwagwarwa sakamkon yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara bakwai da fyade a Unguwar Gwagwarwa da ke birnin Kano.
Kakakin Rundunar ASP Magaji Musa Majiya ya shaida wa Aminiya cewa bisa binciken da rundunarsu ta gudanar an samu jami’in nasu da laifin fayade dumu-dumu, don haka rundunar ta dauki mataskin korarsa daga aikin dan sanda baya ga hukuncin laifin fyade da zai fuskanta a kotu. “Mun gudanar da bincikenmu inda muka samu wannan dan sanda da laifin fyade ga wata yarinya. A lokacin gudanar da binciken mun canja wuri tare da canja wa dan sandan kaya, amma duk da haka yarinyar ta nuna shi a matsayin wanda ya yi mata fyade har ya lalata ta. Yanzu haka rundunarmu ta kore dan sandan daga aiki kuma za a gurfanar da shi gaban kotu don fuskantar hukuncin laifin da ya yi,” inji shi.