An koro daliban Najeriya da ke karatu a Birtaniya

Tashin Dala ya sa ’yan Najeriya kasa biyan kudin makaranta, lamarin da ya sa aka koro su gida daga Birtaniya

An koro daliban Najeriya da ke karatu a Birtaniya

Mummunan karyewar darajar Naira ya shafi daliban Najeriya da ke karatu a Jami’ar Teesside da ke kasar Birtaniya.

Kawo yanzu dai  Jami’ar Teesside ta kado keyar daliban da suka kasa biyan kudin makaranta.

Wasu daga cikin daliban sun shaida wa BBC cewa sun ji takaicin abin da jami’ar ta yi na rashin kulawa da matsalolinsu.

Duk da koke-koke da kokarin da daliban suka yi na yin shawarwari da tsare-tsare na biyan kudin, jami’ar ta kaddamar da tsauraran ka’idojin biza, lamarin da ya sa aka rufe asusun daliban aka kuma soke bizarsu.

Jami’ar ta ce rashin biyan kuɗin makarantar ya saba wa sharuddan bizar da aka ba wa daliban.

Daliban da abin ya shafa sun ce suna cikin tsananin damuwa sakamakon ƙin taimaka musu da jami’ar ta yi; duk da iƙirarin jami’ar ta yi na bayar da taimako ga wasu daga cikinsu.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu