An koya wa masarautu yadda ake sulhu bayan rikice-rikice
Wata kungiyar samar da ci gaba mai suna ‘Green Horizon’ ta kaddamar da taron kwana shida domin koya wa masarautu da masu rike da sarautu hanyoyin gudanar da sulhu bayan rikice-rikice a Karamar Hukumar Girei da ke Jihar Adamawa. Shugabar Kungiyar a Jihar Adamawa, Barista Amina Muhammed Ali ta ce kasancewar masu rike da kananan […]
Wata kungiyar samar da ci gaba mai suna ‘Green Horizon’ ta kaddamar da taron kwana shida domin koya wa masarautu da masu rike da sarautu hanyoyin gudanar da sulhu bayan rikice-rikice a Karamar Hukumar Girei da ke Jihar Adamawa.
Shugabar Kungiyar a Jihar Adamawa, Barista Amina Muhammed Ali ta ce kasancewar masu rike da kananan masarautu na taka rawar gani wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, ya sanya aka kaddamar da taron domin kara musu ilimi wajen magance kananan rikice-rikice a tsakanin jama’a.
Ta ce abu mafi muhimmanci a taron shi ne a kara wa kananan masarautu da masu sarauta ilimi wajen kara fahimtar dokokin da suka shafi samar da zaman lafiya a kasa da sanin hakkin dan Adam da sanin yadda za a yi sulhu ta hanyoyin sauki da kuma kara ilimi wajen yadda za a samar da tsaro a yankunansu.
Shugaban Karamar Hukumar Girei, Alhaji Muhammad Njidda ya ce taron ya zo daidai lokacin da ake bukatarsa domin samar da tsaro da kwanciyar hankali a tsakanin mutane.
Ya ce, kashi 90 na rikice-rikicen da ke faruwa ana samar da sulhu a wajen kananan masarautu don haka taron da kungiyar ta gudanar abin a yaba ne.
Ya shawarci masarautun da su yi amfani da ilimin da aka koyar da su wajen magance rikice-rikice a tsakanin al’ummansu domin samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Ubandoman Adamawa, kuma Jakadan Sulhun Adamawa Dokta Ahmed Ibrahim Mustapha ya ce ya bada goyon bayansa kan wannan tsari, sannan ya ya yi fatar ganin kananan masarautu sun sanya wannan ilimin da aka koyar da su wajen kawo sulhu a tsakanin alummarsu.