An kubutar da 4 daga cikin ma’aikatan kwalejin Osun da aka yi garkuwa
Hukumar ‘yan sanda ta ce, ta ceto ma’aikatan kwalejin fasaha ta jihar Osun hudu da ke garin Esa-Oke, da aka yi garkuwa da su. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun, Mista Fimihan Adeoye ne ya jagoranci kubutar da wanda aka yi garkuwan da su. Ya kuma bayyana wa majiyarmu a Osogbo babban birnin jihar cewa, a […]
Hukumar ‘yan sanda ta ce, ta ceto ma’aikatan kwalejin fasaha ta jihar Osun hudu da ke garin Esa-Oke, da aka yi garkuwa da su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun, Mista Fimihan Adeoye ne ya jagoranci kubutar da wanda aka yi garkuwan da su. Ya kuma bayyana wa majiyarmu a Osogbo babban birnin jihar cewa, a yanzu haka ana kokarin ceto sauran hudun da aka yi garkuwa da su.