An kubutar da barawon malmalar amala daga jarun

Babban Jojin Jihar Oyo, Muntar L. Abimbola ya yi wa wani matashi afuwa, aka sallame shi daga gidan yari, bayan ya kwashe watanni uku a daure saboda kama shi da aka yi da laifin satar malmalar amala day a cinye ta gaya a sakamakon yunwa.Matashin, dan shekara 17 mai suna Moruf Komla, dan kasar Jumhuriyar […]

An kubutar da barawon malmalar amala daga jarun
An kubutar da barawon malmalar amala daga jarun

Babban Jojin Jihar Oyo, Muntar L. Abimbola ya yi wa wani matashi afuwa, aka sallame shi daga gidan yari, bayan ya kwashe watanni uku a daure saboda kama shi da aka yi da laifin satar malmalar amala day a cinye ta gaya a sakamakon yunwa.
Matashin, dan shekara 17 mai suna Moruf Komla, dan kasar Jumhuriyar Benin ne, kamar yadda ya yi wa manema labari jim kadan da fitowarsa daga jarun. Ya bayyana dalilin da ya sa ya share watanni uku jarun.
“Ina zaune ne a wani kauye kusa da garin Ogbomoso sai na rika jin yunwa kamar zan mutu, wanda a nan take da misalin karfe 10 na safe a wannan rana na garzaya zuwa cikin wani gidan makwabta na tambayi wata yarinya cewa ko akwai wani abu da mahaifiyarta ta ajiye da zan iya ci domin maganin yunwa? Yarinyar ta ba ni amsar cewa akwai tuwon Amala amma mahaifiyarta ta fita unguwa. Da na ga ba zan iya jurewa ba sai na fada cikin dakinsu na dauki malmalar amala na cinye ba tare da miya ba, domin yunwar ta dame ni. A lokacin da mahaifiyar yarinyar ta dawo ta samu labari sai ta jagoranci wasu mutane suka yi mani dirar mikiya, suka kai ni ofishin ’yan sanda. Dagan an ne suka kai ni kotu, inda aka tsare ni a gidan yari na tsawon watanni uku,” inji Moruf, wanda ya ce mai gidansa da yake yin aiki a karkashinsa ne ya yi balaguro a daidai lokacin da wannan al’amari ya auku.
Babban Jojin ya yi wa Maruf afuwa tare da sauran fursunoni maza da mata su 107, da ke tsare a gidajen yari na Agodi a Ibadan da Abolongo a garin Oyo. Mafi yawancin wadanda suka samu afuwar sun dade a tsare a gidajen yarin da aka zarge su da aikata kananan laifuka daban-daban da suka kasa cika sharuddan karbar beli.
Jojin wanda ya jagoranci wasu alkalan babbar kotun Ibadan zuwa ziyarar gidajen yarin, a makon jiya, ya bayar da umarnin a sallami mutane 59 nan take daga gidan yari na Agodi Ibadan da mutane 49 daga gidan yari na Abolongo dake Oyo.
A bincikensu, alkalan sun gano cewa akwai mutane da yawa da suka dade a tsare ba tare da yanke masu hukumci ba, wanda yin hakan ya tauye masu hakki ne.