An kubutar da ma’aikatan Jami’ar Abuja daga hannun masu garkuwa da su
An kubutar da su ne da taimakon ‘yan bangar yankin Abaji.
Jami’an ’yan sanda a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja sun sami nasarar kubutar da ma’aikatan da ‘yan bindiga suka sace a rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar Abuja.
Rahotanni sun ce an kubutar da mutanen ne tare da hadin guiwar ’yan bangar yankin Abaji, kan babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja.
- Sarkin Musulmi ya yi wa wanda ya mayar da kudin tsintuwa 19 ta arziki
- Daga Laraba: Me ya sa ake bilichin?
A ranar Talata ne wasu gungun ’yan bindiga suka kai hari jami’ar inda suka yi awon gaba da wasu ma’aikatanta.
Wani ma’aikacin jami’ar ne ya tabbatar da kubutar da mutanen ranar Laraba.
Ya ce an kubutar da su a yammacin ranar Talata da taimakon ’yan sanda da ’yan banga, kuma yanzu haka suna ofishin ’yan sandan na Abaji.
Tun bayan aukuwar lamarin, jami’an tsaro suka ce an samar da babura kusan 13 da kuma motoci ga sojoji domin shiga dajin da ke kusa da makarantar domin neman wadanda aka sace.