An kubutar da shugaban karamar hukuma da dansa

‘Yan sandan jihar Imo sun ceto shugaban karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra Ifeanyi Odimegwu da dansa da direba daga hannun masu garkuwa da jama’a. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Dasuki Galadanchi ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Owerri, inda ya ce, an yi garkuwa da Odimegwu a hanyar Owerri zuwa Fatakwal da safiyar […]

An kubutar da shugaban karamar hukuma da dansa

‘Yan sandan jihar Imo sun ceto shugaban karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra Ifeanyi Odimegwu da dansa da direba daga hannun masu garkuwa da jama’a.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Dasuki Galadanchi ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Owerri, inda ya ce, an yi garkuwa da Odimegwu a hanyar Owerri zuwa Fatakwal da safiyar Lahadi da ta gabata, bayan sun halarci coci a unguwar Elele jihar Ribas.