An kulle Mai unguwa bisa laifin sayar da filayen bogi

Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 3 da ke kofar Kudu cikin Jihar Kano ta garkame wani Mai unguwa bisa samunsa da laifin sayar da filayen bogi ga wani mutum da ke zaune a unguwarsa.dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Garba ya bayyana wa kotu cewa wani mutum mai suna Rabi’u Idris ne ya […]

An kulle Mai unguwa bisa laifin sayar da filayen bogi
An kulle Mai unguwa bisa laifin sayar da filayen bogi

Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 3 da ke kofar Kudu cikin Jihar Kano ta garkame wani Mai unguwa bisa samunsa da laifin sayar da filayen bogi ga wani mutum da ke zaune a unguwarsa.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Yusuf Garba ya bayyana wa kotu cewa wani mutum mai suna Rabi’u Idris ne ya yi kara ga ’yan sanda da ke Gwale, cewa mai unguwar Dabai, Malam Jamilu Garba tare da wani mutum mai suna Abubakar Iliyasu, wanda a yanzu ba a san inda yake ba, cewa sun hada baki sun sayar masa da wasu filaye guda biyar da ke unguwar a kan kudi Naira miliyan biyu da dubu ashirin da biyar, wanda sai daga baya ya gano cewa filayen ba nasu ba ne.
Lokacin da aka karanta masa laifin da ake zarginsa da shi, mai unguwar, wanda a yanzu haka masarautar Kano ta dakatar da shi, ya amsa laifin da ake zarginsa da shi; laifin da mai gabatar da kara ya bayyana cewa ya saba sashe na 120 da 244 da 206 na kundin shari’ar Musulunci ta shekarar 2000.
A cewar mai unguwar: “Wanann magana da aka fadi haka  take sai dai ba ni kadai na ci kudin ba, hasali ma ni Naira dubu 300 kawai na ci a cikin kudin. Sauran mutanen da muka yi wanann abu tare da su, akwai Abubakar Iliyasu da Ibrahim Mu’azzam da Abdulhamid Sharada da kuma Alhaji Auwalu Sharada.”
Har ila yau mai unguwar ya nemi afuwar kotu, a cewarsa ya yi nadamar abin da ya aikata tare da alkawarin ba zai sake aikata irin haka anan gaba ba.
Alkalin kotun mai shari’a Ustaz Ibrahim Sani Sarki Yola ya bayar da umarnin tsare mai unguwar a gidan kurkuku zuwa ranar 18 ga watan da muke ciki, inda za a ci gaba da sauraren shari’ar.
Haka kuma alkalin ya ki yarda da bayar da belin mai unguwar, duk kuwa da kokarin da lauyansa ya yi, inda alkalin ya kafa hujja da cewa bayar da belin mai unguwar zai iya kawo tarnaki ga neman da ake yi wa abokin aikata laifinsa nasa, wato Abubakar Iliyasu wanda ya bace bat a hannun ’yan sanda.