An kunyata masu siyasar addini da kabilanci a Arewa – Barista Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung daya ne daga cikin dattawan Arewa kuma jigo a jam’iyyar APC. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu kan yadda aka gudanar da zabubbukan kasar nan, ya bayyana cewa masu siyasar addini da kabilanci a Arewa sun ji kunya a wadannan zabubbukan da aka gudanar. Kuma masu canza sheka daga jam’iyyar […]

An kunyata masu siyasar addini da kabilanci a Arewa – Barista Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung daya ne daga cikin dattawan Arewa kuma jigo a jam’iyyar APC. A wannan tattaunawar da ya yi da wakilinmu kan yadda aka gudanar da zabubbukan kasar nan, ya bayyana cewa masu siyasar addini da kabilanci a Arewa sun ji kunya a wadannan zabubbukan da aka gudanar. Kuma masu canza sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mutane ne masu neman mukami. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya; Me za ka ce dangane da yadda aka gudanar da zabubbukan kasar nan?

Solomon Dalung; Zabubbukan da aka gudanar a kasar nan a wannan shekara ta 2015, zabubbuka ne da suka zama daban da zabubbukan da aka taba gudanarwa a kasar nan a baya. Domin wadannan zabubbukan sun nuna mutumcin kuri’ar talakawan Najeriya. Kuma sun nuna cewa shi mulkin damakaradiya an girka shi a kan kuri’ar mutane. Domin a wadannan zabubbukan an yi amfani da matakai nagari kuma a karshe aka tabbatar da sakamako nagari. Kuma an kammala wadannan zabubbukan lafiya. Don haka babu shakka wadannan zabubbuka sun kayatar kwarai da gaske kuma sun yi wa shugabanni isharar cewa yanzu talakawa ne ke da iko a mulkin damakoradiya. Domin duk shugaban da ya wulakanta talakawa to su ma za su wulakanta shi.
Aminiya; Ganin yadda a wadannan zabubbuka jam’iyyar APC ta lashe zaben gwamnonin jihohin Filato da Nasarawa da Binuwai. A yanzu za a iya cewa yankin Middle Belt ya dinke da arewacin Nijeriya ke nan?
Solomon Dalung; Dama yankin Arewa a hada yake da yankin Middle Belt, wadansu ne kawai wadanda suke da wata irin akida ta wariya da bambancin addini da kabila suke cin abinci da wannan al’amari na siyasar kananan kabilun Arewa. Sun dade suna cin karensu ba babbaka. Amma a wannan lokaci ganin irin cin zalin da aka yi wa al’ummar Arewa na kashe-kashen mutanensu da kone-konen gidajensu, tun daga jihar Filato zuwa jihar Binuwai da jihar Nasarawa, har ya zuwa jihohin Barno da Yobe da Adamawa, sun dawo daga rakiyar siyasar raba hankalinsu. Yanzu Arewa ta koma matsayinta na baya ta zama tsintsiya madaurinki daya. Mutane guda masu makoma guda. Wannan wani karshe ne na siyasar addini da kabilanci, musamman cin zaben da APC ta yi a jihohin Filato da Nasarawa da Binuwai. Wannan cin zabe ya nuna cewa wadanda suke yawo da wannan akida sun ji kunya.
Aminiya; A matsayinka da lauya me za ka ce dangane da maganar da shugaban kasa Jonathan ya yi na cewa zai mika wa Janar Buhari mulki ne a ranar 28 ga watan Mayu, maimakon ranar 29 ga watan Mayu?
Solomon Dalung; Wato ita gwamnatin Jonathan birgimar hankaka ce, za ka ga baki, za ka ga fari a cikinta, gwamnati ce wadda ta tara wa ‘yan Nijeriya gajiya. A kowanne wayewar gari tana bullo da sababbin abubuwa wadanda a hagunce suke. Don haka wannan magana da Jonathan ya yi bai zamo da mamaki ba. Jonathan da shi da matarsa ne a lokacin da ake yakin neman zabe ya ce ba zai mika mulki ga mutumin da bai kware ba. Duk da kowa ya san Janar Buhari tsohon soja ne wanda ya taba shugabancin kasar nan. Matarsa tana bugun kirji tana cewa duk wanda ya bude baki ya ce canji a jefe shi. Bayan da aka zo aka yi zaben nan da Jonathan ya ga cewa ya fadi, sai ya fito ya ce ya yarda. Yin hakan da ya yi sai wadansu mutane suka fito suna cewa ya nuna bajinta. Sun manta irin tabargazar da ya tafka da irin zagin da ya rika yi wa Janar Buhari.
Don haka wallahi wannan rana ta 28 ga watan Mayu da shugaba Jonathan ya ce zai mika wa Janar Buhari mulki maimakon ranar 29 ga watan Mayu, akwai lauje a cikin nadi. Don haka mu shugabannin adawa za mu je mu nemi madubi, mu duba mu kalli abin da yake cikin wannan shiri da Jonathan yake son ya yi. Domin ba mu yarda da wannan shiri ba, ba za mu yarda a mika mulki a wata rana daban ba. Yaya a lokacin da PDP take satar kuri’a tana mika wa kanta mulki a ranar 29 ga watan Mayu. Bayan mun kayar da su kuma sai su zo su ce za su canza mana ranar da za su mika wa Janar Buhari zuwa 28 ga watan Mayu? Watakila suna neman su shafa mana kashin kaji ne ko kuma wan mummunan fata ne suke son su yi mana.
Sabon zababben shugaban kasar Najeriya Janar Buhari za a rantsar da shi ne a ranar 29 ga watan Mayu kuma za a mika masa mulki a wannan ranar kamar yadda tsarin mulkin kasar nan ya tanada. Domin idan ya karbi mulki a ranar 28 ga watan Mayu an yi wa tsarin mulkin kasar nan zagon kasa. Kuma Janar Buhari mai halin gaskiya ne, don haka ba zai daure wa karya gindi ba.
Aminiya; Ganin yadda wadansu magoya bayan PDP suke ta ficewa daga jam’iyyar suna dawowa jam’iyyarku ta APC, shin kana ganin yin hakan zai kawo cigaban damakoradiya a kasar nan kuwa?
Solomon Dalung; Damakoradiya dai ta gaji jama’a, amma damakoradiya tana tafiya ne da mutane masu alkibla wadanda suka yi imani da alkiblar jam’iyyarsu. Wadanda suke kwararowa zuwa jam’iyyarmu ta APC wadansu ma bayan da suka ga alamar za a kayar da su, sai suka kama gudu zuwa jam’iyyar APC domin su samu matsayi a jam’iyyar. Wadansu ma sai da Janar Buhari ya cinye zaben suka canza sheka zuwa APC. Duk irin wadannan mutane da suka fice daga PDP suka dawo APC akwai alamar tambaya a kansu. Domin mafiya yawansu sun yi aiki da shugaban kasa Jonathan, amma ba su bar gwamnatinsa ba don sun bayar da shawara yaki dauka. Sai bayan da gwamnatin ta kare, ruwa ya cika jirgin, sannan suka canza sheka zuwa APC. Wadansu sun kafa adawa da PDP tun lokacin da gwamnonin nan guda 7 da wadansu ‘yan majalisu suka fara adawa har aka kaita kasa, wadannan ‘yayanmu ne.
Amma masu canza sheka da rana nan suna zuwa jam’iyyarmu ta APC mutane ne wadanda suke son su zo su rikitar mana da wannan amana da ‘yan Najeriya suka ba mu. Masu neman matsayi ne wadanda sun saba da dalolin Amurka da suke rabawa a tsakaninsu.Maimakon su mayar da kudaden da aka sata aka ba su, sai suna ta guduwa suna dawowa jam’iyyar APC.