An kusa ba hammata iska tsakanin magoya bayan ’yan takara a Uyo
A ranar Juma’ar da ta gabata a Uyo Jihar Akwa Ibom lokacin da Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Shiyyar Kudu maso Kudu, magoya bayan ’yan takarar Gwamnan Jihar Kuros Riba a karkashin jam’iyyar wato Ministan Ma’aikarar Neja-Delta, Usani Uguru Uguru da Honarabul John Owan Enoh da suka fafata a zaben […]
A ranar Juma’ar da ta gabata a Uyo Jihar Akwa Ibom lokacin da Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da yakin neman zabensa a Shiyyar Kudu maso Kudu, magoya bayan ’yan takarar Gwamnan Jihar Kuros Riba a karkashin jam’iyyar wato Ministan Ma’aikarar Neja-Delta, Usani Uguru Uguru da Honarabul John Owan Enoh da suka fafata a zaben fid-da-gwani da Owan Enoh ya yi nasara sun yamutsa fuska.
Yadda lamarin ya faru kamar yadda daya daga cikin ’yan jam’iyyar Abdulhak Sani ya shaida wa Aminiya, ya ce “Lokacin da za mu tafi Akwa Ibom taron APC da Shugaban Kasa ya kaddamar da yakin neman zabensa, magoya bayan Usani Usani da na Honarabul John Owan Enoh kowa ya tafi da shaukin cewa nasa gwanin ne Shugaban Kasa zai daga hannunsa ya kuma ba shi tutar jam’iyyar a matsayin dan takara, inda aka ba Owan Enoh tutar jam’iyya wanda hakan ke nufin shi ne dan takara.”
“Ashe lamarin bai yi wa magoya bayan Ministan dadi ba, daga nan sai bangaren John suka fara jifar magoya bayan Usani Usani da ruwan leda. Dama can akwai jikakka tsakanin magoya bayan Usani Usani da na John Owan Enoh, tun lokacin da aka yi zaben fid-da-gwani wanda Owan Enoh ya lashe zaben, shi kuma Ministan ya yi shelar shi ne ya lashe zaben, har abu ya kai su ga zuwa kotu, kuma kamar yadda jam’iyya ta sanar, John Owan Enoh ne dan takararta,” inji shi.
Wannan hayagagar ce ta haifar da rudani, har aka kusa ba hammata iska a dandalin da aka yi taron na APC, amma a karshe ’yan bangaren Usani Usani suka sulale daga daga wurin taron inji shi.