An kusa kawo karshen cutar shan-inna a Kano –Bincike

Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa  al’ummar Jihar Kano suna ba da hadin kai a kokarin da ake yi na tabbatar da  kawar da cutar shan-inna baki daya daga jihar da ma kasa baki daya. Binciken  ya  nuna  cewa iyayen yara da ke yankunan karkara  a  jihar sun  himmatu wajen bayar da […]

An kusa kawo karshen cutar shan-inna a Kano –Bincike
An kusa kawo karshen cutar shan-inna a Kano –Bincike

Wani bincike da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa  al’ummar Jihar Kano suna ba da hadin kai a kokarin da ake yi na tabbatar da  kawar da cutar shan-inna baki daya daga jihar da ma kasa baki daya.
Binciken  ya  nuna  cewa iyayen yara da ke yankunan karkara  a  jihar sun  himmatu wajen bayar da ’ya’yansu ana yi masu allurar rigakafin, tare da kai  su  asibitocin da ke gudanar da allurar lokaci zuwa lokaci.
Sannan ana samun goyon bayan manyan mutane  kan wannan muhimmin aiki na kawar da cutar ta shan-inna kamar limaman manyan masallatai da dagatai da kuma masu unguwanni wadanda suke kokari wajen ganin an cimma nasarar kakkabe wannan cuta kamar yadda aka tsara.
Haka kuma kungiyoyin  da ba na gwamnati ba suna taka muhimmiyar rawa  wajen fadakar da mutane  muhimmancin karbar allurar rigakafin da sauran shirye-shiryen gwamnati da suka shafi kula da lafiyar al’umma.