An kusa rufe amsar labarai a gasar Aminiya

Akalla mutum 218 ne suka turo da labaransu domin shiga gasar rubuta gajerun labarai na Aminiya-Trust. Shugaban Kwamitin Gudanar da Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya ce maza da mata daga sassan Nijeriya da Nijar da kuma kasashen waje, irin su Indiya da China sun turo da labaransu a gasar, wanda ya rage kwana 7 a […]

An kusa rufe amsar labarai a gasar Aminiya

Farfesa Ibrahim Malumfashi

Akalla mutum 218 ne suka turo da labaransu domin shiga gasar rubuta gajerun labarai na Aminiya-Trust.

Shugaban Kwamitin Gudanar da Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya ce maza da mata daga sassan Nijeriya da Nijar da kuma kasashen waje, irin su Indiya da China sun turo da labaransu a gasar, wanda ya rage kwana 7 a rufe amsar labaran.

“Abin da ya kara fitowa fili shi ne yadda aka tallata gasar, wasu sun turo da labarai cikin Ingilishi da fassara da Hausa, wasu kuma a Ingilishi zalla, musamman ganin tallar gasar cikin Ingilishi”, inji shi.

Farfesa Malumfashi ya ce daga cikin wadanda suka shiga gasar akwai wadanda ba Hausawa ba, amma suna jin harshen Hausa, sai dai ba a samu shiga gasar da labaran hadin gwiwa ba.

Daga ranar 16 ga watan Yuli za a fara tantance labaran domin fitar da 15 da za a mika wa alkalai domin fitar da na 1 zuwa na 15 daga cikin labaran da aka turo.

Daga baya kuma za a fitar da zakarun gasar, kamar yadda aka tsara.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno