An kwana ana rawa saboda faduwar Gwamna Darius zaben Sanata a Taraba

Gwamnan ya sha kaye ne a hannun dan takarar APC, David Jumkuta

An kwana ana rawa saboda faduwar Gwamna Darius zaben Sanata a Taraba

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku

Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku ya sha kaye a takaran neman zama Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu a karkashin Jam’iyyar PDP.

Dan takarar Jam’iyyar APC, David Jimkuta ne ya kayar da Gwamnan wanda ke kan gadon mulki.

A cewar jami’in Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ya sanar da sakamakon, Furfesa Solomon Adeyeye daga Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Wukari a Jihar, David Jimkuta ya sami kuri’a 85,415 wanda ya ba shi nasara a kan Gwamna Ishaku da ya sami kuri’a 45,708.

Mazabar dai ta kunshi Kananan Hukumomin Wukari da Ibbi da Ussa da Donga.

A wani labarin kuma, ’yan jam’iyyu daban-daban sun kwana suna ta rawa sabo da murnar faduwar Gwamnan zabe.

Rahotanni daga Wukari da Ibbi da Ussa da kuma Takum, inda nan ne mahaifar Gwamnan, matasa sun kwana suna kade-kade da raye-raye saboda murnar faduwar Gwamnan.

Wadanda wakilinmu ya zanta da su sun ce a shekaru takwas da Gwamnan ya yi yana mulki, bai tsinana wa yankin komai ba.

Wani mai suna Mista James Dauda ya ce ba a taba samun Gwamna wanda bai yi aiki a jihar kamar Darius ba.

Ya ce al’ummar yankin suna da haushin Darius musamman kan kalaminsa na cewa ya kawo masu shinkafa da Magi wai matansu su dafa su ba mazajensu a ranar zabe su zabe shi a matsayin Sanatan da zai wakilce su.