An kwantar da budurwa mai tukuicin mota a asibitin tababbu

Budurwar nan da ta yi shelar bayar da tukuicin mota da gida ga wanda ya zama mijinta Zainab Abdulmalik yanzu haka tana kwance a asibitin masu tabin hankali na Dawanau da ke Kano. Bayanan da Aminiya ta samu daga dangin budurwar da asibtin na Dawanau ya nuna cewa an kwantar da Zainab a asibitin ne […]

An kwantar da budurwa mai tukuicin mota a asibitin tababbu
An kwantar da budurwa mai tukuicin mota a asibitin tababbu

Budurwar nan da ta yi shelar bayar da tukuicin mota da gida ga wanda ya zama mijinta Zainab Abdulmalik yanzu haka tana kwance a asibitin masu tabin hankali na Dawanau da ke Kano.

Bayanan da Aminiya ta samu daga dangin budurwar da asibtin na Dawanau ya nuna cewa an kwantar da Zainab a asibitin ne ranar Lahadin da ta gabata.
A ranar Talatar makon jiya ne Zainab ta shiga gidan Rediyon Freedom ta bayar da sanarwar neman mijin aure tare da bayar da tukuicin mota da gida ga wanda ta zaba a matsayin miji, hakan ya sa washegari Laraba daruruwan matasa suka yi dafifi a kofar gidan rediyon don neman wannan garabasa.
Wani babban ma’aikaci a asibitin ya tabbatar da cewa Zainab na kwance a asibitin, ya cewa ta dade tana karbar magani a asibitinsu. “Wannan ba shi ne karo na farko ake kawo ta asibitin nan ba. Ta dade tana zuwa karbar magani a nan,” inji shi.
Haka wani dan uwanta da ya nemi a boye sunsa ya tabbatar da cewa Zainab tana asibitin saboda rashin lafiyarta ta tabin hankali ta kara tsananta bayan da ta zabi wanda take so daga cikin mutanen da suka yi gangami a gidan rediyon Freedom.
dan uwan nata ya ce rashin lafiyarta ta samo asali ne daga lokacin da wani saurayinta ya yaudare ta bayan ya yi alkawarin zai aure ta tare da karbe mata kudi.
Wani makwabcin su Zainab mai suna Jazuli Rabi’u, ya ce a yanzu haka saurayin da ya yaudare ta an yi kararsa a gaban kotu. “Tare muka taso da ita ba ta da tabin hankali, sai yanzu da wancan saurayinta ya yaudare ta. Ni nakan raka ta gidan iyayen saurayin nata a Gandun Albasa. Yanzu haka an yi kararsa a kotu har ma ya yi alkawarin zai rika biyanta Naira dubu 50 duk wata,” inji shi.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi mahaifinta ya ki cewa komai sai ma tsaki da ya yi ya kashe wayarsa, kuma duk kokarin da ta yi don magana da Zainab ya ci tura saboda ma’aikatan asibitin sun hana ganinta.