An kwaso ‘yan Najeriya 139 da aka kubutar daga gidan yari a Libya

Wadanda lamarin ya shafa sun iso filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

An kwaso ‘yan Najeriya 139 da aka kubutar daga gidan yari a Libya

Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Ci-Rani ta Duniya (IOM) ta kwaso ‘yan Najeriya 139 da aka kubutar da su daga gidajen yarin da aka tsare su a kasar Libya.

Ambasada Kabiru Musa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya mika wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Litinin a Abuja.

Ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da wannan yunkuri don ganin ba a yi watsi da duk wani dan Najeriya da ke tsare a ketare ba saboda laifin yin hijira.

A cewar Musa, wadanda aka kwaso sun hada da maza 85, mata 51, yara biyu da jariri daya kuma sun isa filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas da yammacin ranar Litinin.

Ofishin Jakadancin Najeriya a Libya tare da hadin gwiwar IOM sun sake samun nasarar sako ‘yan ci-rani 139 ‘yan Najeriya da suka yi kaura ba bisa ka’ida ba wadanda aka tsare a kasar Libya.

“Wannan shi ne aiki na uku da muka gudanar a cikin watan da ya gabata, kuma Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen ganin cewa babu wani dan kasar da aka bari a ketare.

“Mutum 139 da aka kwaso sun tashi daga filin jirgin sama na Mitiga, a Tripoli a cikin hayar jirgi mai lamba UZ 0189 da yammacin ranar Litinin kuma sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

“Ba wai kawai mun kwaso su ba ne, mun kuma wayar da musu da kai kan illolin yin hijira ba bisa ka’ida ba, domin su dawo su gargadi wasu dangane da hatsarin da ke tattare da irin wannan tafiya,” in ji Musa.