An kwaso ’yan Najeriya 255 da suka makale a Saudiyya
Gwamnatin Najeriya a ranar Litinin ta sake kwaso karin wasu mutum 255 ’yan kasar da suka makale a kasar Saudiyya. Hukumar kula da ’yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM) ce ta wallafa hakan cikin sako a shafinta na Twitter. Buhari ya taya Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwa Gaskiyar boren sojoji kan yaki da Boko Haram NIDCOM […]
Gwamnatin Najeriya a ranar Litinin ta sake kwaso karin wasu mutum 255 ’yan kasar da suka makale a kasar Saudiyya.
Hukumar kula da ’yan Najeriya mazauna ketare (NIDCOM) ce ta wallafa hakan cikin sako a shafinta na Twitter.
NIDCOM ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja da misalin karfe 1.00 na ranar Litinin.
Hukumar ta ce wani jirgi mai suna Saudi Air Flight SV3405 ne ya yi dakon ’yan Najeriyar zuwa gida wadanda su ne rukuni na farko.
Kai tsaye za su wuce zuwa sansanin Alhazai na Abuja inda za a killace sun a tsawon kwana 14 kamar yadda ka’idodin mahukunta masu yaki da cutar Coronavirus suka tanadar.
Sannan ta ce akwai wani rukunin na ’yan Najeriya da su na nan tafe a nan gaba.