An kwato gari na karshe a Yobe daga Boko Haram
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayar da sanarwar kwato garin Goneri gare na karshe da ke hannun kungiyar Boko Haram a Jihar Yobe. Jami’an tsaron hadin gwiwa masu kula da aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Yobe (JTF) ne suka samu nasarar kwato garin Goneri da ya rage a hannun mayakan kungiyar kwanaki kadan da […]
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayar da sanarwar kwato garin Goneri gare na karshe da ke hannun kungiyar Boko Haram a Jihar Yobe.
Jami’an tsaron hadin gwiwa masu kula da aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Yobe (JTF) ne suka samu nasarar kwato garin Goneri da ya rage a hannun mayakan kungiyar kwanaki kadan da kwato garin Buni Yadi fadar karamar Hukumar Gujba daga hannun ’yan Boko Haram.
Wata sanarwa da Kakakin Hedkwatar Tsaro ta kasa Manjo Janar Chris Olukolade ya fitar ta ce, sojojin da ke yaki da ’yan kungiyar Boko Haram sun fatattaki ’yan kungiyar daga Goneri da ya rage wa ’yan kungiyar sakamakon ba-ta-kashi da suka suka yi.
Goneri dai gari ne da ke da muhimmanci ga ’yan Boko Haram kasancewarsa mahada da Gabas da shi kadan za a tarar da dajin da ke shiga Sambisa.
Wani daga cikin maharban da ke aiki da jami’an tsaro lokacin da suka kai harin kwato Goneri da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa sun yi gumurzu da ’yan bindigar kafin su samu nasara a kansu. Y ace mayakan Boko Haram suna da miyagun makamai to amma jami’an tsarontsun fatattake su tare da kashe da dama daga cikinsu.
A makon jiya ne dai sojoji suka kai hari ga mazaunin mayakan Boko Haram da ke garin Yadin Buni, inda suka sake kame garin tare da gano wata ma’aikatar hada bama- bamai a kamfanin takin zamani na Jihar Yobe da ke garin Gujba.