An kwato motocin alfarma 50 daga mata da jami’an gwamnatin Yuguda

Kwamitin da Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya kafa domin kwato wasu daga cikin kayayyakin da jami’an tsohuwar gwamnatin Malam Isa Yuguda suka wawushe ya samu nasarar kwato motocin alfarma 25 da matan tsohon Gwamna Isa Yuguda suka wawushe da kuma wasu 25 daga jami’ansa. Shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Baba ya bayyana wa wakilinmu cewa […]

An kwato motocin alfarma 50 daga mata da jami’an gwamnatin Yuguda
An kwato motocin alfarma 50 daga mata da jami’an gwamnatin Yuguda

Kwamitin da Gwamnan Jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya kafa domin kwato wasu daga cikin kayayyakin da jami’an tsohuwar gwamnatin Malam Isa Yuguda suka wawushe ya samu nasarar kwato motocin alfarma 25 da matan tsohon Gwamna Isa Yuguda suka wawushe da kuma wasu 25 daga jami’ansa.

Shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Baba ya bayyana wa wakilinmu cewa matan Gwamna Yuguda uku sun dawo da motoci kirar jeep-jeep da 406 da Toyota Camry da sauran manyan motoci masu tsada.
A cewarsa akwai daya daga cikin matan da har yanzu ba ta dawo da motocin da ta yi awon gaba da su ba, amma sun samu labarin cewa ba ta Najeriya ta yi tafiya zuwa kasar waje ne.
To, sai dai kuma wasu majiyoyi sun tsegunta wa wakilin Aminiya cewa Hajiya Nafisa Yuguda ’yar marigayi Shugaban kasa Umaru ’Yar’aduwa ce ba ta dawo da motocinta ba.
Shugaban kwamitin ya ce ya kamata al’umma su fahimci cewa suna wannan aiki ne tsakaninsu da Allah ba domin tozarta wani ba, kuma duk wanda ya saci dukiyar al’umma zamansa lafiya ya dawo da abin da ya dauka.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa akwai manyan jannaretoci da wasu daga cikin kwamishinonin tsohuwar gwamnatin suka yi awon gaba da su kuma nan ba da jimawa ba za su kwato sauran kayayyakin.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan aikin kwamitin, Shugaban Jam’iyyar NDP reshen Jihar Bauchi Malam Abubakar dandada ya ce Gwamna Abubakar ya yi zurfin tunani da ya kafa kwamitin, ya ce duk wanda ya saci dukiyar al’umma ya dawo da abin da ya dauka, ya ce da dama daga cikin wadanda aka ba su amanar dukiyar al’umma a tsohuwar gwamnatin su yi sata har da na rashin kunya.
Ya bukaci al’ummar jihar su bayar da goyon bayan da ya kamata ga kwamitin domin ta haka ne za su sauke nauyin da aka dora musu.