An kwato shanu dubu biyu daga barayin shanu a Birnin Gwari

Jami’an tsaron hadin gwiwa a Jihar Kaduna sun yi nasarar kashe wadanda ake zargin barayin shanu ne su uku kuma suka kama tara a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar.Jami’an tsaron wadanda suka hada da sojin kasa da na sama da ’yan sanda da na tsaron farin kaya (SSS) da sauransu sun kuma yi […]

An kwato shanu dubu biyu daga barayin shanu a Birnin Gwari
An kwato shanu dubu biyu daga barayin shanu a Birnin Gwari

Jami’an tsaron hadin gwiwa a Jihar Kaduna sun yi nasarar kashe wadanda ake zargin barayin shanu ne su uku kuma suka kama tara a karamar Hukumar Birnin Gwari da ke jihar.
Jami’an tsaron wadanda suka hada da sojin kasa da na sama da ’yan sanda da na tsaron farin kaya (SSS) da sauransu sun kuma yi nasarar kwato shanu dubu biyu da ake zargi na sata ne.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i wanda ya ziyarci yankin tare manema labarai ya isa garin Damari da Birnin Gwari don gane wa idonsa wadanda aka kama da kuma shanun da aka gano.
Gwamna El-Rufa’i ya yaba wa sojin da sauran jami’an tsaron kan wannan nasara da suka samu a yankin,  ya ce an dade jama’ar yankin na fama da ayyukan ’yan ta’adda.
A cewarsa, hadin gwiwar jami’an tsaron na ci gaba da ayyukansu a jihohin Neja da Katsina da Zamfara da kuma Kebbi domin kakkabe sauran ’yan ta’addan.
“Muna alfahari da ayyukan da sojojin kasar nan da sauran jami’an tsaro suke yi na kokarin kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a yankin nan wadanda suka dade suna addabar jama’a. Wannan matsala ta dade a yankin saboda haka muke kira ga jama’a su ci gaba da yi wa jami’an tsaron nan addu’a domin samun nasarar kawo karshen wannan matsala,” inji Gwamnan
Ya kara da cewa: “Wannan aikin tsaro na hadin gwiwa ne da ke faruwa a dazukan jihohin Kebbi da Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja inda ’yan ta’adda ke addabar mutanen yankin. Sojojin kasa da na sama da ’yan sanda da jami’an SSS da Cibil Defence duk suna cikin wannan aiki.”
Kyaftin A. Ujah, wanda shi ne ya yi jawabi a madadin shugaban jami’an tsaron da kula da wannan aiki Birgediya Janar .S. Malu, ya ce akalla yan ta’adda tara suka kama yayin da uku suka rasu a yayin musayar wuta a tsakaninsu.
Ya ce suna ci gaba da wannan aiki kuma suna fatar cin nasara wajen kawo karshen ayyukan ’yan ta’adda a yankin.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne gwamnonin jihohin Kebbi da Zamfara da Neja da Katsina suka wani taro a Kaduna domin tattauna yadda za su kawo karshen sace-sacen shanu da ayyukan ’yan ta’adda a dajin yankin na Birnin Gwari da ya yi iyaka da jihohin nasu.