‘An lalata galibin Masallatai a Afirka ta Tsakiya’

Jakadar kasar Amurka a Majalisar dinkin Duniya Samantha Power ta ce an lalata galibin Masallatai da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sakamakon rikicin da aka shafe fiye tsawo fiye da shekaru biyu. Samantha Power wadda ta ziyarci Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a makon da ya gabata, ta ce masallatai 19 ne kacal suka rage daga […]

‘An lalata galibin Masallatai a Afirka ta Tsakiya’
‘An lalata galibin Masallatai a Afirka ta Tsakiya’

Jakadar kasar Amurka a Majalisar dinkin Duniya Samantha Power ta ce an lalata galibin Masallatai da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sakamakon rikicin da aka shafe fiye tsawo fiye da shekaru biyu.

Samantha Power wadda ta ziyarci Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a makon da ya gabata, ta ce masallatai 19 ne kacal suka rage daga cikin fiye da 436 da ake da su a kasar. Lokacin da ta ziyarci wata unguwar kusa da babban birnin kasar, Bangui wadda kuma galibin mazaunanta Musulmi ne, ta bayyana unguwar da “al’ummar da ke rayuwa a cikin dimuwa.”
Mrs Power ta bayyana damuwa a kan yadda lamarin tsaro zai kasance idan dakarun kasar Faransa da na Tarayyar Turai suka fice daga kasar.
Rikicin kasar ya janyo mutuwar dubban mutane da kuma hasarar dimbin dukiya, tun bayan da kasar ta fada yaki a karshen shekarar 2013. Wannan ya sa mutane fiye da miliyan hudu kauracewa muhallansu . Kuma galibin wadanda suke gudun hijirar Musulmai ne.