An mai da fulani saniyar ware a Kebbi – Sajo

Wani Shugaban Fulani a Jihar Kebbi, Alhaji Sajo Sabbi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta gaggauta samar da burtalin kiwon dabbobi a dukkannin kananan hukumomin Jihar 21da kuma tabbatar da isasshen tsaro ga al’ummar Fulani don dorewar zaman lafiya anan Jihar Kebbi. Alhaji Sajo Sabbi ya yi wannan kiran ne a lokacin […]

An mai da fulani saniyar ware a Kebbi – Sajo

Wani Shugaban Fulani a Jihar Kebbi, Alhaji Sajo Sabbi ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta gaggauta samar da burtalin kiwon dabbobi a dukkannin kananan hukumomin Jihar 21da kuma tabbatar da isasshen tsaro ga al’ummar Fulani don dorewar zaman lafiya anan Jihar Kebbi.

Alhaji Sajo Sabbi ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a Birnin Kebbi fadar Gwanatin Jihar Kebbi, Alhaji Sajo ya   bayyana cewa al’ummar Fulani sun yi makukar damuwa dangane da yawaitar arangamar da ake samu a tsakanin manoma da kuma   makiyaya Fulani, ko kuma fadawa Fulani da wasu al’umma ke yi a cikin dare suna kone masu gidaje da dabbobi wanda kai tsaye ya danganta hakan da gazawar Gwamnatin Jihar Kebbi da kuma na  kananan hukumomi, inda ya bada misali da abinda ya faru a karamar hukumar Suru a  kwanakin baya, a inda al’ummar wani kauye suka far ma fulani suka kone masu gidajensu da dabbobinsu, ba gaira ba dalili. A cewarsa rashin isasshen burtali na kiwo a Jihar Kebbi na daga cikin matsalolin da suka kai wa samu mummunar tashin-tashina a tsakanin al’ummar Fulani da kuma sauran kabilu.

A bisa haka ne ya yi kira ga majalisar dokokin Jihar Kebbi da su hanzarta amincewa da dokar samar da burtali a fadin Jihar Kebbi. Alhaji Sajo, ya kuma kara da cewa al’ummar Fulani su ne masu bada gudummuwa mafi tsoka wajen havvaka tattalin arzikin kasa musamman ma ta fuskar bada kudaden shiga da kuma samar da dabbobi, a bisa haka akwai bukatar dake akwai ga gwamnati da su samar ma su da dukkanin kariyar rayukansu da dukiyoyinsu.

Ya ce “Wace kabila ce mafi amfani ga Jihar nan? Wallahi zaka ga Fulani ne, amma mene ne ake mana?” Sannan ya kalubalanci Gwamnatin Jihar Kebbi da cewa su bayyana abu guda daya tak da suka yi wa Fulani, zaka ji an raba taki ga manoma, shin ka tava jin wani abu ga Fulanin Jihar Kebbi? A cewarsa.