An maida dokar hana fita zuwa dare a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sassauta dokar hana fita zuwa dare a manyan biranen jihar. Mai taimakawa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, akan watsa labarai, Samuel Aruwan ya ce an sassauta dokar hana fita a jihar, inda dokar zata fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba. Aruwan ya ce, an […]

An maida dokar hana fita zuwa dare a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sassauta dokar hana fita zuwa dare a manyan biranen jihar.

Mai taimakawa Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, akan watsa labarai, Samuel Aruwan ya ce an sassauta dokar hana fita a jihar, inda dokar zata fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba.

Aruwan ya ce, an sassauta dokar ne bayan ganawar da shugabannin tsaro suka yi a jihar inda suka baiwa Gwmnatin jihar shawarar sassauta dokar hana fitan.