An maka dan takarar gwamnan PDP na Katsina a Kotu kan kudin zabe

Jam’iyyar PDP na da tsagi biyu a jihar; wanda kowane ke ikirarin shugabancinta.

An maka dan takarar gwamnan PDP na Katsina a Kotu kan kudin zabe

Yayin da ake tunkarar zaben gwamnoni, wani tsagi na jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ya maka dan takarar gwamnan jam’iyyar, Yakubu Lado Danmarke, a kotu kan zargin sama da fadi da kudin zabe Naira biliyan 1.05.

Sauran wadanda karar sun hada da mataimakin dan takarar gwamnan, Aminu Ahmed Yar’dua, Shugaban Kungiyar Lado na jihar, Lawal Danbaci da Babban Daraktan yakin neman zaben Atiku da Lado na jihar, Dokta Mustapha Muhammad Inuwa da sauransu.

Shugaban PDP na jihar, Lawal Uli da wasu mutum 13 ne suka shigar da karar madadin jam’iyyar suna neman a ba su izinin neman bayani kan yadda aka raba kudi Naira biliyan 1.05 da aka ware don hidimar zaben shugaban kasa na 2023 da aka yi ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa kotun ta karbi kokensu a ranar Talata, amma ba ta bayar da ranar da za a saurari wannan batu ba.

Jam’iyyar PDP ta rabu gida biyu a Jihar Katsina, kuma kowane tsagi na ikirarin shugabancin jam’iyyar.