An maka ECOWAS a kotu kan shirin yaki a Nijar

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta je kotu neman umarnin dakatar da shirin ECOWAS na yakar gwamnatin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar

An maka ECOWAS a kotu kan shirin yaki a Nijar

Masu zanga-zangar kyamar Faransa da goyon bayan juyin mulki a Nijar a yayin tattakin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kasarsu a ranar 3 ga Agusta, 2023. (Hoto: / AFP)

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa ta je kotu domin neman umarnin dakatar da shirin kungiyar ECOWAS na kaddamar da yaki a kasar Nijar inda sojoji suka yi juyin mulki.

Kungiyar Egalitarian Mission for Africa (EMA) ta bukaci kotun ta ECOWAS ta dakatar da kungiyar daga shirintta na fada wa sojojin Nijar da yaki.

EMA wadda lauyan Najeriya Kayode Ajulo ke jagoranta, ta bayyana wa kotun cewa abin da ECOWAS ke shirin yi haramun ne, domin ya saba wa yarjejeniyarta da ta haramta mata far wa kasashenta.

Sauran wadanda suka hada gwiwa wajen shigar da karar sun hada da wani lauya daga Arewacin Najeriya mai suna Hamza Dantani da tsohon shugaban cibiyar harkokin cikin gida ta Najeriya (NIIA) Farfesa Bola Akinterinwa.

Wadanda ake karar su ne kungiyar ECOWAS, hukumar shugabannin kasashe da gwamnatocin ECOWAS da shugaban wakilan ECOWAS da kuma gwamnatocin Najeriyya da Nijar.

Dokar kungiyar ta wajabta cewa duk lokacin da aka shigar da kara a gaban kotun, to ya zama wajibi bangarorin da abin ya shafa su dakata daga daukar duk wani mataki. Kawo yanzzu dai kotun ECOWAS ba ta sanya ranar fara sauraron karar ba.

Juyin mulkin Nijar

A ranar 26 ga watan Yuli Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban Kasar Nijar, Janar Abdourhamane Tchiani ya yi wa zababben shugabna kasa Mohammed Bazoun juyin mulki tare da ci gaba da tsare shi.

A ranar Talata ECOWAS ta yi barazanar sanya wa gwamnatin sojin Nijar sabbin takunkumai, bayan wa’adin da ta ba wa sojojin na mika wa Bazoum mulki ya cika ba tare da sojojin sun yi abin da kungiyar ta bukata ba.

ECOWAS na duba yiwuwar daukar matakin soji a Nijar, amma gwamnain sojojin kasar ta ce ba za ta raga wa duk wanda ya yi yunkurin keta hurumin kasarsu ba.

Hasali ma, sun katse hulda babbar makwabciyar kasarsu, Najeriya da ke jagorantar ECOWAS, da kuma Togo, Amurka da Farasa, tare da rufe sararin samaniyar kasarsu sai abin da hali ya yi.

ECOWAS za ta yi sabon zama a ranar Alhamis domin cimma ma matsaya kan matakinta na gaba a Nijar.

Shugaban Najeria Bola Tinubu, wanad kuma shi ne shugaban kwamitin shugabannin kasashen ECOWAS, ya lashi takobin daukar duk matakan da suka kamata na ganin Bazoum ya dawo kan mulki.

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Mahara sun kai wa Sarkin Nupen Lokoja hari a fadarsa

Gwamnati ta ba da hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara

NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Suke Haddasa Turmutsutsu A Najeriya