An maka Sarkin Dutse a gaban kotu kan rabon gadon mahaifinsa

Matar tsohon Sarkin ce ta maka shi a gaban kotun kan gadon wani gida

An maka Sarkin Dutse a gaban kotu kan rabon gadon mahaifinsa

Daya daga cikin matan marigayi Sarkin Dutse, Asiya Nuhu Sanusi, ta maka Sarki mai ci, Hamim Nuhu Sanusi, a gaban kotun daukaka ta Musulunci a kan rabon gado.

A kwafin karar, wacce lauyanta, Barista Abdullahi Ali ya shigar, matar marigayin da wasu mutum bakwai, suna kalubalantar Sarkin mai ci, wanda dan marigayin ne kan wani hukunci da wata kotu ta yanke a baya.

A cewarsu, hukuncin da Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke a kan batun gadon iyalan mamacin akwai kuskure a cikin shi.

A cikin karar mai lamba SCAJG/CV/2023, Asiya ta bukaci kotun ta sake bincika ko akwai kuskure a hukuncin kotun baya a kan wani gida mai lamba 17 JGNL/DU/RES/94/264, wanda ta ce marigayin ya ba ta tun yana da rai, amma aka raba gado da shi.

Ta ce sai da ta gabatar da shaidar da take tabbatar da mallakarta ga gidan, amma aka ki la’akari da ita.

Karar ta ce marigari Sarkin ya ba kowacce daga cikin matansa kyautar gidaje guda biyu, amma kotun ta amince da shaidar sauran matan ta tabbatar musu da nasu, ita kuma aka raba nata a cikin kayan gado.

Ka kafa hujja da sashe na 36 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da wasu ayoyin Alkur’ani a kan rabon gado, tana mai rokon kotun daukaka karar da ta jingine hukuncin baya.

Marigayi Nuhu Muhammadu Sanusi dai ya rasu ne ranar 30 ga watan Janairun bana, inda ya bar mata biyu da ’ya’ya 13.

Akwai kuma wata matar tashi da suka rabu da ita tun kafin rasuwarsa.

Da wakilinmu ya bincika kotun da aka shigar da karar a Dutse, babbar birnin Jihar Jigawa, wani rajistara a kotun da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida masa cewa ba a kai ga sanya ranar fara sauraron karar ba.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya