An mayar da Gaza maƙabarta mafi girma a duniya — EU

Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya kai 31,923.

An mayar da Gaza maƙabarta mafi girma a duniya — EU

Babban jami’in kula da harkokin waje na Tarayyar Turai (EU), Josep Borrell  ya bayyana cewa, yaƙin da sojojin Isra’ila ke yi a Gaza ya mayar da yankin ya zama maƙabarta mafi girma a duniya.

“Gaza ta kasance tana da babban gidan yari mafi girma kafin fara yaƙin. A yau ita ce maƙabarta mafi girma a duniya, “in ji Borrell a taron ministocin EU a Brussels.

“Wata maƙabarta ce ga dubun dubatar mutane da kuma maƙabarta ga yawancin muhimman ƙa’idojin dokar jin ƙai.”

Borrell ya kuma sake nanata zarginsa da cewa Isra’ila na amfani da yunwa a matsayin “makamin yaƙi” ta hanyar ƙin barin manyan motocin agaji shiga Gaza.

“Isra’ila na amfani da matakin haifar da yunwa,” in ji shi a wani taron jin ƙai.

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Isra’ila Katz, ya mayar wa Borrell martani, ya kuma ce masa da ya daina kai wa Isra’ila hari, mu kuma amince da ‘yancinmu na kare kai daga laifukan Hamas.

“Isra’ila ta ba da damar kai agajin jin ƙai mai yawa zuwa Gaza ta ƙasa, da sama da ruwa ga duk wanda ke son taimakawa,” in ji Katz kamar yadda ya bayyana kafar sadarwar zamani X (twitter).

Yaƙin Gaza mafi muni da aka taɓa yi ya ɓarke bayan da Ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar da wani harin da ba a taɓa ganin irinsa ba, a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 1,160 a Isra’ila, galibi fararen hula, a cewar ƙididdigar da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya bayar bisa alƙaluman hukumomin Isra’ila.

Mayaƙan Islama sun kuma yi garkuwa da kusan mutane 250 da Isra’ila ta yi amanna cewa 130 sun rage a Gaza, ciki har da 33 da ake kyautata zaton sun mutu.

Isra’ila, ta lashi takobin ruguza Hamas tare da kuɓutar da mutanen da aka kama, ta kai wani harin bam ba tare da ɓata lokaci ba, da kuma farmakin ƙasa da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce ta kashe aƙalla mutane 31,726, yawancinsu mata da yara.

Ƙasashe 27 na EU sun yi ta kokawa kan yadda za su mayar da martani bai ɗaya kan yaƙin Gaza yayin da wasu ƙasashe ke marawa Isra’ila baya wasu kuma na goyon bayan Falasɗinu.

Ministocin Tarayyar Turai sun shirya tattaunawa kan shawarar da Ireland da Spain suka gabatar na dakatar da yarjejeniyar haɗin gwiwa da Isra’ila, amma da wuya wannan matakin ya samu goyon bayan dukkanin ƙasashe 27.

Sai dai ana sa ran EU za ta amince da takunkumin da aka ƙaƙaba wa Hamas kan cin zarafin mata a ranar 7 ga watan Oktoba da kuma kan ‘yan Isra’ila masu tayar da ƙayar baya a Yammacin Kogin Jordan saboda kai wa Falasɗinawa hari.

Tuni dai Biritaniya da Amurka suka ƙaƙaba takunkumin da aka ƙaƙaba wa wasu ‘yan ta’adda masu tsatsauran ra’ayi.

Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya kai 31,923

A ranar Laraba Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ce, adadin waɗanda suka mutu a hare-haren Isra’ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 31,923 da mutum 74,096 da suka jikkata.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe Falasɗinawa aƙalla 104 tare da jikkatar 162.