An mayar da Gidan Dambe na Abuja Masallacin Juma’a

Fitaccen gidan damben nan na Abuja da ke garin Deidei da wasu gidaje biyu da a baya aka yi amfani da su a matsayin gidan karuwai da kuma masaukin baki duk a garin Deidei da ke karamar Hukumar Bwari a yankin Birnin Tarayya Abuja, an maida su Masallacin Juma’a. Hakan ya faru ne bayan da […]

An mayar da Gidan Dambe na Abuja Masallacin Juma’a
An mayar da Gidan Dambe na Abuja Masallacin Juma’a

Fitaccen gidan damben nan na Abuja da ke garin Deidei da wasu gidaje biyu da a baya aka yi amfani da su a matsayin gidan karuwai da kuma masaukin baki duk a garin Deidei da ke karamar Hukumar Bwari a yankin Birnin Tarayya Abuja, an maida su Masallacin Juma’a. Hakan ya faru ne bayan da wani mazaunin yankin Dokta Muhammad bin Muhammad Alkwandawi Sarkin Malaman Deidei ya saye su ya gina masallaci.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka yi bikin bude masallacin tare da mika shi ga kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah don kulawa da shi.
Bikin bude masallacin ya samu halartar dimbin jama’a da suka jawo tsaiko a garin na tsawo lokaci, kuma Sakataren kungiyar Izala ta kasa, Sheikh Muhammad Kabir Gombe ne ya wakilci shugaban kungiyar ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau.
A jawabinsa Sheikh Kabir Gombe ya bayyana al’amarin a matsayin sadakatul jariya tare da kira ga masu sukuni su yi koyi da Sarkin Malaman.
Sheikh Abdurrazak Yahaya Haifan wanda aka ba rikon Limancin Masallacin tare da nauyi sama masa limami na dindindin ne ya jagoranci Sallar Juma’a ta farko a ranar.
Daga cikin mahalarta taron har da wasu tubabbun tsagerun matasa sama da 100 da Alkwandawi ya sama musu sana’a, a gidajen sayar da abinci da makarantu da cibiyoyin kasuwanci, bayan sun rasa ayyukan yi, sakamakon saye wuraren da suke gudanar da miyagun sana’o’insu a garin na Deidei da ya yi, tare da gina wuraren da suke aikin a yanzu.
A ganawarsa da Aminiya bayan bude masallacin, Dokta Muhammad Alkwandawi, ya ce “Na yanke shawarar sayen wurin in maida shi masallaci ne bayan na yi la’akari da irin ayyukan masha’a da ake aikatawa a wurin, inda hakan ke barazana ga zaman lafiya a garin tare da birnin tarayya gaba daya. Wurin nan ya kasance inda ake sayar da miyagun kwayoyi iri-iri ga masu sari, inda matasanmu da wasu daga cikinsu ’yan mata ne da suka guje wa iyayensu ke kara-kaina, baya ga hayaniyar da suke jawowa ga mazauna garin a yayin hidimominsu da ke gudana cikin dare.”
Dokta Alkwandawi ya kuma ce ya yanke shawarar gina masallacin ne don magance matsalar husuma da ke faruwa a ranakun Juma’a sakamakon hadewar sahu a tsakanin masallacin Izala da na darika a garin.