An mayar da Hama Amadou kurkuku
A ranar Litinin da safe ne madugun ’yan hamayyar Jamhuriyar Nijar Alhaji Hama Amadou, ya gabatar da kansa gaban kotun Yamai wadda ta yanke masa hukuncin zaman kaso na shekara daya. Tuni aka mayar da shi gidan kaso na Flingue (Filinge) da ke Jihar Tillabery a ranar Litinin din, inda daga can ne ya tafi neman […]
Alhaji Hama Amadou
A ranar Litinin da safe ne madugun ’yan hamayyar Jamhuriyar Nijar Alhaji Hama Amadou, ya gabatar da kansa gaban kotun Yamai wadda ta yanke masa hukuncin zaman kaso na shekara daya.
Tuni aka mayar da shi gidan kaso na Flingue (Filinge) da ke Jihar Tillabery a ranar Litinin din, inda daga can ne ya tafi neman magani Faransa a shekarar 2016 bai dawo ba.
Hama zai cike wata takwas ne don cika adadin zaman da kotu ta yanke masa. Sai dai mutanen kasar na tunanin Shugaban Kasar Mahammadou Issoufou zai yi wa Hama Amadou afuwa ganin yanayin da ake ciki.
Ko Shugaban ya yi masa afuwa ba za ta yi tasiri ba ga makomar siyasar Hama idan aka yi la’akari da ayar kundin zaben kasar mai lamba 47 da ta haramta wa wanda ya fuskanci daurin shekara daya ya yi takara.
A makon jiya ne Hama ya koma kasar bayan ya kwashe fiye da shekara biyar yana gudun hijira a kasar Faransa.
Hama Amadou, wanda tsohon Firayi Ministan kasar ce, ya gudu daga kasar bayan da aka bankado badakalar safarar jarirai daga Najeriya, inda aka zarge shi da hannu ciki a watan Agustan shekarar 2014.
Wane ne Hama Amadou?
An haifi Hama Amadou a 1950 a garin Youri da ke Jihar Tillabery.
Ya yi karatun aikin Kwastam da na gwamnati a Makarantar Koyon Aikin Gwamnati (ENAM) da ke Birnin Yamai da kuma Babbar Cibiyar Koyon Aikin Gwamnati ta Duniya da ke birnin Paris na Faransa.
Hama Amadou ya rike manyan mukaman gwamnati da dama daga 1972 zuwa 1988, lokacin da ya zama Ministan Watsa Labarai.
A lokacin Babban Taron Kasar a1991, Hama Amadou ya tsaya kai-da-fata wajen kare Jam’iyyar MNSD-Nasara, wadda ya wakilta a wajen taron, abin da ya ba shi damar zama Babban Sakatarenta a 1991.
Amadou ya yi Firayi Minista tsakanin 1995 da 2007, inda Majalisar Dokokin Nijar ta kada kuri’ar yanke kauna a kansa.
A shekarar 2008 hukumomi sun kulle shi a gidan kurkukun Koutoukale inda ya shafe wata 10 bisa zargin cin hanci. Daga bisani ya fice daga Jam’iyyar MNSD-Nasara ya kafa jam’iyyarsa ta MODEN-Lumana. Sau uku kuma ana zabarsa a matsayin dan Majalisar Dokoki.
A zaben Shugaban Kasa na 2011 ya zo na uku, kuma ya mara wa Mamahadou Issoufou baya a zagaye na biyu. Hakan ya sa ya samu mukamin Shugaban Majalisar Dokoki har zuwa 2014, lokacin da ya fice daga kasar saboda zargin da yake fuskanta na hannu a wata badakala ta sayo jarirai daga Najeriya.
An kama shi yayin da ya koma gida a watan Nuwamban 2015, kuma aka tsare shi a kurukukun Fillingue.
A watan Satumban 2015 ne, jam’iyyarsa ta MODEN-Lumana ta tsaida shi dan takarar Shugaban Kasa a zaben da aka yi a watan Fabrairun 2016.