An mayar da mu saniyar-ware – kungiyar AOPSHON
kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare na yankin Arewacin Najeriya, wacce atakaice ake kira (AOPSHON), ta bayyana takaicinta dangane da yadda wasu gwamnatocin jihohi suka mayar da mambobinsu saniyar ware a yankin Arewa.Mataimakin sakataren kungiyar reshen Arewacin Najeriya, Kwamared Ya’u TK Isa Bauchi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya ta wayar salula a […]
kungiyar Shugabannin Makarantun Firamare na yankin Arewacin Najeriya, wacce atakaice ake kira (AOPSHON), ta bayyana takaicinta dangane da yadda wasu gwamnatocin jihohi suka mayar da mambobinsu saniyar ware a yankin Arewa.
Mataimakin sakataren kungiyar reshen Arewacin Najeriya, Kwamared Ya’u TK Isa Bauchi ne ya yi furucin yayin da yake tattaunawa da Aminiya ta wayar salula a karshen makon da ya gabata.
Kwamared Ya’u ya bayyana cewa mambobinsu sun zama abin tausayi saboda bambancin da ake nuna musu.
Ya ce gwamnonin jihohin Arewa da yawa sun ki su biya mambobinsu albashin watannin masu yawa.
“Gaskiya ana nuna mana bambanci. Jihohi da yawa sun ki su biya mambobinmu albashi. Wasu jihohin suna bin bashin watannin hudu wasu kuwa watannin biyar kai har watanni shida wasu jihohin suke bin gwamnatocinsu,” inji shi.
Ya dage a kan cewa malaman makaranta su ne suke karbar mafi karancin alabashi wanda ba ya isar su daukar dawainiyar iyalansu.
A cewarsa malami ya zama abin tausayi saboda rashin albashi mai tsoka da kuma jinkirin da ake samu wajen biyansa albashi.
Ya bayar da misali da Jihar Bauchi inda ya ce suna bin gwamnatin jihar bashin albashin watan Janairu.
Ya ce idan gwamnati ta ci gaba da tafiya haka to babu shakka ba za ta cimma burinta na samar da ingantaccen ilimi a kasar nan ba.
Ya ce dole sai gwamnati ta kara albashin malamai tare da biyansu a kan lokaci muddin tana so ta yi maganin tabarbarewar ilimi a yankin Arewa.
Ya bayyana cewa babu yadda za a yi malami ya koyar ko kuma shugaban makaranta ya sanya ido sosai a kan malamansa muddin gwamnati ba ta biyansu albashin da ya dace ba.