An mayar wa Shugaban karamar Hukumar Kaduna ta Arewa kujerarsa

Shugaban Gwamnatin Rikon kwarya na karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, wanda gwamnatin jihar ta dakatar daga bakin aiki, Alhaji Ahmed Kurfi ya koma bakin aikinsa a ranar Talatar nan da ta gabata.Wannan ya biyo bayan wasika mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Balarabe Abbas Lawal, mai dauke da kwanan wata na 13 Nuwamba […]

An mayar wa Shugaban karamar Hukumar Kaduna ta Arewa kujerarsa
An mayar wa Shugaban karamar Hukumar Kaduna ta Arewa kujerarsa

Shugaban Gwamnatin Rikon kwarya na karamar Hukumar Kaduna ta Arewa, wanda gwamnatin jihar ta dakatar daga bakin aiki, Alhaji Ahmed Kurfi ya koma bakin aikinsa a ranar Talatar nan da ta gabata.
Wannan ya biyo bayan wasika mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Balarabe Abbas Lawal, mai dauke da kwanan wata na 13 Nuwamba 2015 ta bayar da umurnin yin haka. Wasikar ta ba da umurnin a gaggauta mayar da shi bakin aikinsa ba tare da bata lokaci ba.
Idan ba a mance ba, an dakatar da shugaban karamar hukumar ne a ran 8 ga watan Octoban bana, a sakamakon yin gaban kansa wajen daukar mataki dangane da kokarin gwamnatin jihar na karbo filayen gwamnati da wasu suka mamaye.
Bayan an dakatar da shi, an kuma binciki halayyarsa kuma an gayyace shi da ya zo domin amsa wasu tambayoyi. An yi la’akari da amsoshinsa da kuma sakamakon karshen bincikensa da aka yi, inda aka gano cewa dole a yaba masa dangane da kokarinsa na yaki da rashin gaskiya. Sai dai kuskuren da aka samu wajen tafiyar da kuma zartar da aikin abin bacin rai ne.
Binciken da aka aiwatar ya wanke Shugaban karamar hukumar daga kowank irin zargi, sannan aka yaba masa a kan jajircewarsa wajen yaki da rashin gaskiya.
A saboda haka ne gwamnati ta ga ya dace a dage masa wannan dakatar da shi da aka yi domin ya samu damar komawa bakin aikinsa. Sai dai kuma wasikar ta bukaci shugaban ya zama mai kula da ka’idojin aiki sannan kuma gwamnatin ta sake jaddadawa ma’aikatan gwamnati da su rika bin doka da oda wajen gudanar da aikinsu.