An miƙa wa Majalisar Kano ƙorafin ƙara wa’adin manyan ma’aikatan gwamnati

Gwamna Yusuf ya amince da ƙarin wa’adin shekaru biyu ga Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, wasu Manyan Sakatarori.

An miƙa wa Majalisar Kano ƙorafin ƙara wa’adin manyan ma’aikatan gwamnati

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.

A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu.

A cikin wata wasika mai kwanan wata 6 ga Janairu, 2025, Sani Usman DanAbdullo, Esq., Daraktan Gudanarwa da Harkokin Gabaɗaya na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), ya buƙaci Majalisa da ta kare doka da oda, tare da dakatar da abin da ya bayyana a matsayin rashin amfani da ikon zartarwa yadda ya kamata.

An aike da ƙorafin ne zuwa ga Kakakin Majalisar, Hon. Jibrin Ismail Falgore, da kuma Shugaban Kwamitin Majalisa kan Ƙorafe-ƙorafe na Jama’a.

Takardar ta ƙalubalanci Dokar Zartarwa da aka fitar a ranar 1 ga Janairu, 2025, wadda ake zargi da bayar da ƙarin shekaru biyu ga Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Magatakardan Majalisa, wasu alƙalai, da ma’aikatan ɓangaren lafiya.

Ana iya tuna cewa Gwamna Yusuf ya amince da ƙarin wa’adin shekaru biyu ga Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, wasu Manyan Sakatarori, da manyan ma’aikatan gwamnati, wanda zai fara aiki daga 31 ga Disamba, 2024.

Gwamnan ya kare wannan mataki, yana mai cewa Dokar Buƙatar Dole (Doctrine of Necessity) ce ta tilasta hakan, yana mai dogaro da sassa 5(2) da 208 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999.

Sai dai a cikin ƙorafin, an bayyana cewa wannan umarni ya ci karo da dokokin jihar, musamman Dokar Fansho da Giratuti ta Jihar Kano (Gyara Na 5), 2024, wadda ta tanadi shekarun ritaya su kasance shekara 60 ko shekaru 35 na aiki.

Ƙorafin ya jaddada cewa umarnin zartarwa ba domin soke doka ba ne, balle gyaranta, sai dai aiwatar da ita.

Bugu da ƙari, mai ƙorafin ya yi watsi da dogaron gwamnan kan Dokar Buƙatar Dole, yana mai bayyana hakan a matsayin maras inganci a doka da harkokin gudanarwa.

Ya gargaɗi cewa wannan umarni na iya haifar da rikice-rikicen gudanarwa, zarge-zargen nuna wariya, da kuma ƙarar da ka iya gurgunta tafiyar da mulki.

Har ila yau, ƙorafin ya caccaki tsarin zaɓaɓɓen ƙarin wa’adin ga wasu mutane kawai, yana mai cewa Jihar Kano na da ƙwararrun ma’aikata da za su iya maye gurbin waɗanda wa’adinsu ya ƙare, ba tare da karya doka ba.

DanAbdullo ya buƙaci Majalisa da ta yi amfani da ikon sa ido da take da shi, domin soke wannan dokar zartarwa.

Ya yi gargaɗi cewa idan ba a yi hakan ba, hakan na iya zama tushen matsala da zai lalata tsarin aikin gwamnati a Kano.

Dangote ya karya farashin man fetur

An miƙa wa Majalisar Kano ƙorafin ƙara wa’adin manyan ma’aikatan gwamnati

Matasa 150 Sun Halarci Gasar Kirkire-Kirkiren Fasaha a Kano

APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar