An mika ragamar shugabancin masallacin Unguwar Hausawa a Ribas
Basaraken Owerewere da ke Karamar Hukumar Abua/Odual a Jihar Ribas kuma jagoran Kungiyar Jama’atu Nasril Islam da Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a jihar, Alhaji Hamza Diama Honour Eziwas ya nuna jin dadinsa kan mika takardun mallakar Masallacin Rumuokurushi ga al’ummar Musulmin jihar. Alhaji Hamza Diama wanda marigayi Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido […]
Lokacin da ake miqa takardun masallacin Ribas
Basaraken Owerewere da ke Karamar Hukumar Abua/Odual a Jihar Ribas kuma jagoran Kungiyar Jama’atu Nasril Islam da Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a jihar, Alhaji Hamza Diama Honour Eziwas ya nuna jin dadinsa kan mika takardun mallakar Masallacin Rumuokurushi ga al’ummar Musulmin jihar.
Alhaji Hamza Diama wanda marigayi Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido ya nada ya jagoranci kungiyoyin Musulmin biyu a matsayinsa na dan kasa a shekarar 2006, ya halarci mika masallacin ne da iyalan marigayi Malam Mohammed Egweteny ta hannun dansa Ahmed Mohammed Egweteny suka mika wa Sarkin Hausawa Alhaji Isa Madaki.
An sanya hannu a kan takardun tun 1985 da aka sanya hannu a tsakanin mai sayarwa da al’ummar Musulmi Jihar Ribas.
An mika hoton takardun ga kwamitin masallacin yayin da aka mika takardun asali ga Alhaji Isa Madaki Sarkin Hausawa a matsayinsa na mai rikon amanar al’ummar Musulmin
A tattaunawa da Aminiya Alhaji Halliru Imam Sarkin Malaman Jihar Ribas, ya ce, makasudin taron da suka yi na mika takardun masallacin ga kwamitin an yi ne, don ci gaba da ayyukan masallacin.
Alhaji Halliru, ya ce masallacin wanda aka yi shi sama da shekara 30, Sarkin Hausawa na daya daga cikin wadanda suka sanya hannu aka samu takardar mallakarsa. Kuma wanda takardar ke hannunsa tun asali ya rasu, daga hannun ’ya’yansa aka karbo shi ne ya sa suka karbo don yi musu ayyuka. Saboda idan ba takardun aikin ba zai yiwu ba. To yanzu shi ne Sarki ya karbo takardar tunda girma ya zo masa, ya mika wa dansa ragamar takardun masallacin a gaban kwamitin masallacin domin a ci gaba da duk abin da ake son yi.
Alhaji Halliru, ya bayyana abubuwan da filin masallacin ya kunsa kamar, shi kansa masallacin da makaranta da dakin liman da wajen alwala da famfo da ban-daki da ake samun dan kudin shiga daga cikinsa. “Wannan masallaci ya kai sama da shekara 30 a Unguwar Rumuokurushi a Fatakwal, amma karkashin Karamar Hukumar Abua/Odual,” inji shi.