An mika sunayen kwamashinoni ga Majalissar Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakatr ya mika sunayen mutum 13 ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa da su domin nada su a matsayin kwamishinonin jihar. Kakakin Gwamnan Malam Bello Muhammad Zaki ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.Wadanda aka aika […]

An mika sunayen kwamashinoni ga Majalissar Jigawa
An mika sunayen kwamashinoni ga Majalissar Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakatr ya mika sunayen mutum 13 ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da amincewa da su domin nada su a matsayin kwamishinonin jihar.
Kakakin Gwamnan Malam Bello Muhammad Zaki ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Talatar da ta gabata.
Wadanda aka aika sunayen nasu sun hada da Barista Sani Husaini Garun Gabas da Injiniya Aminu Usman Yakubu da Hajiya Rabi Is’hak da Ibrahim Garba Hannun-Giwa da Ahmed Muhammed babura.
Sauran sun hada&nbsp da Dokta Abba Zakari da Umar Maddi da Malam Kabiru Ali da Adamu Sarki Miga da Bala Ibrahim Mamsa da Hajiya Ladi dansure da Alhaji Barau Gambasha da kuma Aminu Sidi ’Yanleman.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista