An muttsuke mutane a wasan mawakin Najeriya a Landan
Daruruwan masoyan fitaccen mawakin Najeriya Asake da wandonsa ya yage yana tsaka da wasa a Landan sun yi kutsen harabar da ya ke waka, in da suka mutsuttsuke mutane
Daruruwan masoyan fitaccen mawakin Najeriya Asake da wandonsa ya yage yana tsaka da wasa a Landan sun yi kutse a harabar da yake gudanar da waka, inda suka muttsuke mutane.
Magajin Garin Landan, Sadiq Khan, ya bayyana damuwarsa kan kutsen da ya auku ranar Alhamis a gidan rawa na O2 Academy, tare da godiya ga jami’an agaji da suka garzaya wurin domin dakatar da masu kutsen da suka yi sanadiyar turmutsutsin.
’Yan sanda da jami’an lafiya da jami’an kashe gobara ne suka isa wurin domin dakatar da mutanen da kuma bai wa wadanda suka samu raunuka agaji.
Magajin garin ta shafinsa na Twitter ya ce al’ummar kasar su kwantar da hankalinsu, domin suna gudanar da bincike.
“Ina jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, musamman mutane takwas din da ke kwance a asibiti, da kuma hudun da ba su san inda kansu yake ba.
“Mun tura rundunar tsaro ta musamman don binciko wadanda suka yi wannan aika-aika, musamman ganin wadanda suka raunata matasa ne masu jini a jika.
“Muna kira ga duk wanda ke da bayani kan wadannan mutane ya yi gaggawar sanar da mu, don hankalinmu ba zai kwanta ba, har sai mun tabbatar an hukunta su,” in ji shi.
Lamarin ya faru ne lokacin da mawakin ke tsaka da waka a dandamali, inda wasu matasa da yawa marasa tikitin shiga dandalin suka rika dannowa harabar ta karfi da yaji, har sai da ’yan sanda suka dakatar da wasan.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutum kusan 3,000 ne suka yi kokarin kutsawa cikin kofofin gidan wasan.