An naɗa Alhaji Mohammed Abubakar sabon Chokalin Fika

NUJ ta mika sakon taya murna ga Alhaji Mohammed Abubakar bisa nadin Chokalin Fika.

An naɗa Alhaji Mohammed Abubakar sabon Chokalin Fika

Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu IIdriss

Mai Martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Ibn Abali Muhammadu Idrisa CON, CFR, ya nada Alhaji Mohammed Abubakar a matsayin sabon Chokalin Fika.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Masarautar Fika ta fitar a ranar Juma’a, 28 ga watan Yunin 2024.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mukaddashin Sakataren Masarautar Fika, Alhaji Ali Gimba Fika ta ce nadin ya fara aiki nan take.

Ana sa ran Alhaji Mohammed Abubakar, wanda ke zama abokin huldar kafafen yada labarai ga Sarkin na Fika, zai kawo kwarewarsa a sabon mukaminsa na Chokalin Fika.

Alhaji Mohammed Abubakar, sabon Chokalin Fika

Majalisar Masarautar ta taya Alhaji Abubakar murnar nadin da aka yi masa tare da yi masa fatan samun nasara a kan sabon mukamin nasa.

Ana kallon wannan nadi a matsayin wani muhimmin ci gaba a harkokin gudanar da Masarautar Fika, kuma masu ruwa da tsaki na da kwarin guiwar tasirin da zai yi ga al’umma.

Kungiyar wakilan kafofin yada labarai (Correspondent Chapel) da ke karkashin Kungiyar ’yan Jarida ta Kasa (NUJ) reshen Jihar Yobe, ta mika sakon taya murna ga Alhaji Mohammed Abubakar bisa nadin da aka yi masa a matsayin sabon Chokalin Fika.

A cikin wata takarda da shugaban kungiyar, Ahmed I Abba da sakataren kungiyar, Michael Oshomah suka sanyawa hannu, sun bayyana fatan alheri ga Alhaji Abubakar a kan sabon mukaminsa.