An naɗa mace ta farko shugabar sojojin Kanada

Naɗin na Carignan ya zo ne lokacin da sojoji ke fuskantar ƙalubalen ƙara yawan kuɗaɗen tsaro.

An naɗa mace ta farko shugabar sojojin Kanada

Laftanar-Janar Jennie Carignan

Kanada ta naɗa Laftanar-Janar Jennie Carignan a matsayin mace ta farko Shugabar Hafsan Tsaro ta kasar.

Firayiminista Justin Trudeau ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.

Carignan, wanda a halin yanzu take aiki a matsayin babbar jami’ar ɗa’a da al’adu, za ta maye gurbin Janar Wayne Eyre, wanda zai yi ritaya.

Ta kai shekaru 35 tana yi wa ƙasar hidima har zuwa sabon aikinta. Ta jagoranci sojoji ƙasashen: Afganistan da Bosnia da Iraki, da Siriya, kuma an santa da irin jagoranci na musamman da sadaukarwa.

Firayiminista Trudeau ya kasance mai ba da shawara mai ƙarfi don daidaiton jinsi, inda a shekarar 2018 ya naɗa Brenda Lukki a matsayin mace ta farko shugabar ’yan sandan Royal Canadian Mounted.

Naɗin na Carignan ya zo ne a wani lokaci mai mahimmanci ga sojoji, wanda ke fuskantar ƙalubale irin su ƙara yawan kuɗaɗen tsaro da magance baɗala da rashin ɗa’a.

A matsayinta na sabuwar Hafsan Hafsoshin Tsaro, za ta ɗauki nauyin jagorantar ƙoƙarin da sojoji ke yi na magance waɗannan matsalolin.

An haifi Carignan a Asbestos, da ke Ƙuebec, mahaifinta ɗan sanda ne kuma mahaifiyarta  malama ce.

Ta shiga aikin soja ne a shekarar 1986, kafin a ba mata damar shiga fagen fama. Ta sami horo a matsayin injiniyar yaƙi, mai share bama-bamai da gine-gine. Ta ta tabbatar da kanta a cikin fagen daga.