An naɗa ni minista don ƙwato wa APC Kano — Ata

Sabon ministan ya ce zai tabbatar APC ta sake ƙwace Jihar Kano a zaɓen 2027.

An naɗa ni minista don ƙwato wa APC Kano — Ata

Sabon Ƙaramin Ministan Gidaje da Ci Gaban Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya ce an naɗa sa minista ne don ƙwato wa jam’iyyar APC Jihar Kano a shekarar 2027.

Ata, ya bayyana haka ne yayin ziyararsa ta farko zuwa Kano bayan shiga Majalisar Zarstawa ta Tarayya.

Yayin da yake magana da ’yan jarida, ya ce, “Naɗina ya fi shafar siyasa. APC ta rasa Jihar Kano, kuma yanzu za ta karɓe jihar. Babbar matsalar da za mu fuskanta tana Kano ta Tsakiya, kuma ni daga nan na fito.”

Ya ƙara da cewa, “Ko da ni minista ne, zan ci gaba da zama cikin wannan yanki. Za mu yi aiki tuƙuru domin ganin APC ta karɓe ikon Jihar Kano kafin 2027.”

Ata, ya bayyana cewa burinsa ya fi shafar siyasa, duk da cewa zai mayar da hankali kan aikinsa a ma’aikatar gidaje da ci gaban birane.

“Zan yi aikina, amma zan riƙa dawowa Kano a kowane mako domin aikin da aka ba ni wajen cimma wannan buri,” in ji shi.

Ya gode wa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa naɗin da ya masa.

Ya ce muƙamin da aka masa ba shi kaɗai ya shafa ba har da al’ummar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

“Wannan shi ne tabbacin da na bai wa Shugaban Ƙasa,” in ji Ata.

“A shekarar 2027, Kano za ta koma ƙarƙashin ikon jam’iyyar APC.”