An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo
Yaƙi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 7,000 a wannan shekarar.

An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a ƙasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta ɓarke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Kongo.
Ƙungiyoyin raya ƙasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuraɗiyyar Kongo inda yaƙi ya ƙazanta a gabashin ƙasar.
- Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi
- 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa
Shugabanin ƙasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi naɗin a wani yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin basasa a gabashin Kongo, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da hukumomi na gwamnatin tsakiya.
Da yammacin jiya Litinin, suka fitar da sanarwar cewa sun naɗa tsohon shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da tsohon Firai Ministan Habasha, Hailemariam Desalegn da kuma tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo a matsayin waɗanda za su taimaka wajen aiwatar da sabuwar yarjejeniyar sulhu.
“An buƙaci dukkan ɓangarorin su mutunta tsagaita wutar da aka ayyana a taron EAC da SADC, kuma an yi kira ga M23 da kuma sauran ɓangarorin su dakatar da kutsawa cikin gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo tare da mutunta tsagaita wuta,” in ji ƙungiyoyin a wata sanarwar da suka fitar.
Har yanzu ƙungiyoyin kasa da kasa da suka haɗa da Majalisar Dinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU sun gaza shawo kan rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongon wanda ya laƙume rayukan fararen hula da dama.
Yaƙi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 7,000 a wannan shekarar, kamar yadda Firaiministar ƙasar Judith Suminwa Tuluka ta shaida wa kwamitin kare haƙƙin ɗan’adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Litinin.