Lamiɗon Adamawa ya naɗa hakiman riƙo 32
Majalisar Sarakunan Jihar Adamawa ta sanar naɗin sababbin hakimai 32 a matsayin na riƙo.
Majalisar Sarakunan Jihar Adamawa ta sanar naɗin sababbin hakimai 32 a matsayin na riƙo.
Majalisar Sarakunan, wadda Lamiɗon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkinɗo Aliyu Mustapha Barkinɗo, yake jagoranta ta sanar da sunayen dagatan ne a cikin wata takarda.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun Kabiru Bakari, wanda shi ne Tariya Adamawa, ta ce an naɗa hakiman ne a sabbin yankunan hakiman da gwamnatin jihar ta kirkira.
Sanarwar bayyana cewa ba a ayyana sunan hakiman riƙo da aka nada a yankunan Murke da Sate ba, sai nan gaba.