An naɗa sabon Magatakardan Zazzau

Zuwa gaba za a sanar da ranar da za a yi bikin yi wa sabon Magatakardan na Zazzau naɗin rawani.

An naɗa sabon Magatakardan Zazzau

Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya

Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya amince da naɗin Alhaji Yusuf Abubakar Hayatu a matsayin sabon Magatakardan Zazzau.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da al’umma na Masarautar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya raba wa manema labarai a Zaria.

Kwarbai ya ce zuwa gaba za a sanar da ranar da za a yi bikin yi wa sabon Magatakardan na Zazzau naɗin rawani.

Sabon Magatakardan Zazzau wanda kuma shi ne Sakataren Masarauta, jika ne ga marigayi Sa’in Zazzau kuma babban ɗan Sarkin Sudan na Zazzau, Alhaji Abubakar Hayatu.

Sabon Magatakardan mai shekaru 48, ya shafe fiye da shekaru 21 yana aikin gwamnati da ma’aikatu masu zaman kansu.

Ya soma aiki ne a matsayin jami’im shige da ficen kuɗi na Hukumar Tsaro ta Sibil Difens daga shekarar 2003 zuwa 2004.

Daga shekarar 2004 zuwa 2006, ya yi aiki matsayin manajan hulɗa na Banki FSB Plc.

Haka kuma, sabon Magatakardan Zazzau ya yi aiki a matsayin manajan a Bankin Oceanic daga shekarar 2008 zuwa 2009.

Daga watan Janairu zuwa Disamban shekarar 2012, ya yi aiki a matsayin manajan gudanarwa da harkokin kuɗi a Kamfanin Gidan Gona na Premium Poultry Farms Ltd.

Alhaji Abubakar Hayatu ya kuma yi aiki a matsayin jami’in tsare-tsaren karɓar haraji a Jihar Kaduna.

Ya yi karatu a fannin lissafin kuɗi a Jami’ar Bayero da ke Kano, sannan a watan Mayun 2022 ya dawo Masarautar Zazzau a matsayin sakatarenta.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan