An naɗa Sarkin Muri Shugaban Kwamitin Farfaɗo da Harkokin Noma a Taraba

Alhaji Abbas Tafida manomi ne mai himma kuma madugun masu da’awa kan ayyukan noma na zamani.

An naɗa Sarkin Muri Shugaban Kwamitin Farfaɗo da Harkokin Noma a Taraba

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya naɗa Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njidda Tafida a matsayin shugaban kwamitin da aka ɗora wa alhakin farfaɗo da harkokin noma a jihar.

Haka kuma, gwamnan ya naɗa wasu Sarakunan gargajiya 9 na jihar a matsayin mambobin kwamitin.

Alhaji Abbas Tafida manomi ne mai himma kuma madugun masu da’awa kan ayyukan noma na zamani.

Kwamitin, a cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Yusuf Sanda ya fitar, ana sa ran zai samar da tsare-tsare da nufin kara inganta harkokin noma da samar da abinci a jihar Taraba.

Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin ya shirya tsaf domin samar da sabbin hanyoyin warwarewa da kuma dabarun tunkarar kalubalen da ake fuskanta a fannin noma a jihar.