An nada Aishatu Abubakar Hashidu Sarauniyar Hashidu
Mai Martaba Hakimin garin Hashidu dake karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Adamu, ya nada Hajiya Aishatu Abubakar Habu Hashidu (Iyami) Babbar ‘yar tsohon gwamnan farko na farar hula a Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Habu Hashidu, Sarauniyar Hashidu. Da take nuna farin cikinta kan wannan nadin sarauta da aka mata a lokacin […]
Mai Martaba Hakimin garin Hashidu dake karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Adamu, ya nada Hajiya Aishatu Abubakar Habu Hashidu (Iyami) Babbar ‘yar tsohon gwamnan farko na farar hula a Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Habu Hashidu, Sarauniyar Hashidu.
Da take nuna farin cikinta kan wannan nadin sarauta da aka mata a lokacin da take zantawa da Aminiya, Hajiya Aishatu Abubakar Hashidu, ta ce irin gudumawar da take bayarwa ne ga al’umma da kuma Masarautar Hashidu ya sa Hakimin ya nada ta a matsayin Sarauniya.
Hajiya Aishatu ta ce kasancewar su ‘yan garin Hashidu tun farko lokacin suna kanana, mahaifinsu ya nuna mu su cewa ba su da wani gari da ya wuce Hashidu, tun daga lokacin suke son garin a ransu suka kuma martaba shi.
Ta kara da cewa, a matsayinta ta Mai Baiwa Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo shawara, tana amfani da wannan damar wajen isar ma sa matsalolin garin nasu, wanda ta dalilinta an samu cigaba sosai wadda al’ummar garin da ma yankin suke alfahari da ita.
“Mahaifinmu ya bada gudumawa sosai a garin Hashidu tun a lokacin da yake minista a lokacin mulkin soja na Ibrahim Babangida, domin shi ne ya samar wa da garin ruwan sha kafin ya zama gwamna, wanda mu ma da muke ‘ya’yansa muka bada irin tamu gudumawar da ya dora mu akan tafarkin,” inji Sarauniyar.
Sarauniyar Hashidu ta ce akwai abubuwa da dama da ta yi don kashin kanta na samarwa da matasa aikin yi tare da bai wa kungiyar kwallon kafa rigunan wasa (Jersey) da kwallaye da sauran abubuwa wadanda idan bukatar hakan ta taso take yi ba tare da sai an nemi ta yi ba.
Hajiya Iyami, kasancewar yanzu ta zama Sarauniya ta kara da cewa yanzu ba sai an nema ba, duk abunda ta ga ya dace za ta ci gaba da hada kai da gwamnati dan ganin an ciyar da Masarautar Hashidu da yankin karamar Hukumarsu ta Dukku gaba, ba tare da an abar su a baya ba.
Daga nan sai ta yi amfani da wannan damar ta godewa Allah (SWT) da ya nufi Hakimin Hashidu, Alhaji Abubakar Adamu ya zabo ta cikin dubban mutane ya nada ta wannan sarauta, inda kuma nan ne mahaifarta.
Sannan sai ta yi kira ga sauran masu hannu da shuni musammam ‘yan garin Hashidu da su zo a hada kai wajen ganin an ciyar da Masarautar da Matasan garin Hashidu gaba.