An nada Alhaji Abdullahi Mustapha a matsayin Sarkin Akunza
Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai na II ya nada Yariman Akunza-Jarme Alhaji Abdullahi Idris a matsayin sabon Sarkin Akunza-Jarme inda ya gaji mahaifinsa Alhaji Mustapha Umaru wanda ya rasu kimanin wata uku da suka gabata. Da yake jawabi bayan nadin, Sarkin Lafiya ya shawarci sabon sarkin ya jagoranci al’ummarsa cikin gaskiya da […]
Mai martaba Sarkin Lafiya Alhaji Isa Mustapha Agwai na II ya nada Yariman Akunza-Jarme Alhaji Abdullahi Idris a matsayin sabon Sarkin Akunza-Jarme inda ya gaji mahaifinsa Alhaji Mustapha Umaru wanda ya rasu kimanin wata uku da suka gabata.
Da yake jawabi bayan nadin, Sarkin Lafiya ya shawarci sabon sarkin ya jagoranci al’ummarsa cikin gaskiya da rikon amana ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba. Kuma ya yi kira ga al’ummar Akunza-Jarme su ci gaba da zaman lafiya da junansu kuma su ba sabon sarkin cikakken goyon baya don samun nasarar sauke nauyin da aka dora masa.
A jawabin Madakin Lafiya Alhaji Isiyaka Dauda ya ya bukace shi ya tabbatar ya tafi tare da al’ummarsa don samun ci gaba da zaman lafiya a yankin.
A jawabin godiya, Alhaji Abdullahi Idris ya jinjina wa masarautar Lafiyakan nada shi inda ya yi alkawarin dorawa daga inda marigayi Sarki Mustapher Umaru ya tsaya. Ya bukaci abokan takararsa su hada hannu don samun zaman lafiya da ci gaban yankin.