An nada dan Arewa mashawarcin Gwamnan Kurosn Riba

Daga cikin nade-nade da bayar da muqaman gwamnati da sakatarori da mashawarta na musamman, Gwamnan Jihar Kuros Riba Farfesa Ben Ayade ya nada Barista Musa Maigoro a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin baqi, wadanda ba ’yan asalin jihar ba.Tun farko Gwamnan ya dauki alqawari matuqar ya kafa gwamnati, idan ya zo nada muqamai, […]

An nada dan Arewa mashawarcin Gwamnan Kurosn Riba
An nada dan Arewa mashawarcin Gwamnan Kurosn Riba

Daga cikin nade-nade da bayar da muqaman gwamnati da sakatarori da mashawarta na musamman, Gwamnan Jihar Kuros Riba Farfesa Ben Ayade ya nada Barista Musa Maigoro a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin baqi, wadanda ba ’yan asalin jihar ba.
Tun farko Gwamnan ya dauki alqawari matuqar ya kafa gwamnati, idan ya zo nada muqamai, zai nada dan Arewa a matsayin mai ba shi shawara, lamarin da yanzu ya cika alqawari.
Barista Musa ne, dan siyasa kuma dan kasuwa da ke zaune a garin Ikom, daya daga cikin manyan biranen Jihar Kuros Riba.
Idan za a iya tunawa, lokacin da Gwamnan ya gana da ’yan Arewa kafin ya zama Gwamna lokacin a sakatariyar Qaramar Hukumar Kalaba, ya ce a ba shi sunan wani wanda zai nad a shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar idan ya kafa gwamnati, yanzu haka lamarin da ake jira shi ma a ga wanda za a nada.