An nada Dittuwa Ardon Ardodin Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka a Jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Alhaji Muhammad Bello Adam (Dittuwa) a matsayin ardon ardodin masarautar Saminaka a wani biki da aka gudanar a fadarsa a ranar Asabar din makon jiya.Da yake jawabi a lokacin nadin Alhaji Musa Muhammad Sani ya cewa sun yi nadin ne domin su […]

An nada Dittuwa Ardon Ardodin Saminaka

Mai martaba Sarkin Saminaka a Jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Alhaji Muhammad Bello Adam (Dittuwa) a matsayin ardon ardodin masarautar Saminaka a wani biki da aka gudanar a fadarsa a ranar Asabar din makon jiya.
Da yake jawabi a lokacin nadin Alhaji Musa Muhammad Sani ya cewa sun yi nadin ne domin su nuna wa duniya cewa masarautar Saminaka tana tare da al’ummar Fulani.
Ya ce akwai gundunomi uku da suka hada da Maskawa da Lazuru da Juran Kari a masarautar Saminaka wadanda dukkansu Fulani ne suke rike da hakimcinsu su. Ya ce Fulanin da suke masarautar suna zaune lafiya da sauran al’ummomin masarautar.
Sarkin ya ce sabon ardon yana da kyakkyawar dangantaka da dukan al’ummar Fulanin masarautar, don haka aka nadi shi a kan wannan sarauta.
Ya yi kira ga al’ummar Fulani da suke masarautar su ci gaba da zaman lafiya da sauran al’ummar yanki kamar yadda suke yi a yanzu.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan kammala nadin Ardon Ardodin Alhaji Muhammadu Dittuwa ya gode ga Sarkin kan wannan nadi da aka yi masa. Kuma ya gode wa al’ummar Fulanin yankin kan goyan baya da hadin kan da suka ba shi kan nadin da aka yi masa.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar Fulanin yankin kan su hada kai su zauna lafiya kuma su kai ’ya’yansu makaranta domin su samu cigaba.
Bikin nadin ya samu halartar ardodin Fulani da sauran al’ummar Fulani daga wurare daban-daban na kasar nan.