An nada Dokta Ibrahim Baninge Sarkin Maganin Ningi

Mai martaba Sarkin Ningi da ke Jihar Bauchi Dokta Yunusa Muhammad danyaya  yanada mai maganin gargajiyar nan da ke zaune a Jos Jihar Filato Dokta Muhammad Ibrahim Baninge a matsayin Sarkin Maganin Masarautar Ningi a ranar Asabar da ta gabata a fadarsa da ke garin Ningi.Da yake jawabi a wajen Sarkin Ningi Dokta Yunusa danyaya […]

An nada Dokta Ibrahim Baninge Sarkin Maganin Ningi
An nada Dokta Ibrahim Baninge Sarkin Maganin Ningi

Mai martaba Sarkin Ningi da ke Jihar Bauchi Dokta Yunusa Muhammad danyaya  ya
nada mai maganin gargajiyar nan da ke zaune a Jos Jihar Filato Dokta Muhammad Ibrahim Baninge a matsayin Sarkin Maganin Masarautar Ningi a ranar Asabar da ta gabata a fadarsa da ke garin Ningi.
Da yake jawabi a wajen Sarkin Ningi Dokta Yunusa danyaya ya ce ya nada Sarkin Maganin ne saboda ganin cancantarsa. Don haka ya yi kira a gare shi kan ya rike wannan amana da aka ba shi, ta hanyar ba da gudunmawarsa wajen ganin an dada bunkasa wannan sana’a ta magungunan gargajiya a masarautar.
Sarkin ya yi kira ga masu magungunan gargajiya na masarautar su ba sabon sarkin maganin goyan baya da hadin kai kuma su rike wannan sana’a da gaskiya.
Daga nan ya yi kira ga al’ummar masarautar su hada kansu su ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu. Ya ce yin hakan ne zai dada bunkasa wannan masarauta.
Da yake zantawa da wakilinmu, bayan kammala nadin sabon Sarkin Maganin na Ningi Dokta Ibrahim Baninge ya nuna matukar farin cikinsa da wannan nadi da aka yi masa.
Ya ce babu shakka wannan wata dama ce da aka ba masu maganin gargajiya a wannan masarauta don inganta wannan sana’a ta maganin gargajiya.
Ya ce zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin an inganta sana’ar magungunan gargajiya a masarautar, inda ya yi kira ga masu maganin gargajiya na masarautar su ba shi goyon
baya da hadin kai.
Bikin nadin ya samu halartar manyan mutane da masu magungunan gargajiya daga wurare daban daban na kasar nan.