An nada farar fata shugaban riko a Zambiya

An nada mataimakin Shugaban kasar Zambiya Guy Scott a matsayin shugaban riko bayan rasuwar Shugaban kasar Michael Sata ranar Talatar da ta gabata, a wani asibitin birnin Landan. Ministar Tsaron kasar Edgar Lungu ya ce Mista Scott zai ci gaba da rike mukamin ne kafin gudanar da zabe cikin kwana 90. Bayan hakan zai mika […]

An nada farar fata shugaban riko a Zambiya
An nada farar fata shugaban riko a Zambiya

An nada mataimakin Shugaban kasar Zambiya Guy Scott a matsayin shugaban riko bayan rasuwar Shugaban kasar Michael Sata ranar Talatar da ta gabata, a wani asibitin birnin Landan.

Ministar Tsaron kasar Edgar Lungu ya ce Mista Scott zai ci gaba da rike mukamin ne kafin gudanar da zabe cikin kwana 90. Bayan hakan zai mika mulki ga dan takarar da ya samu nasara a zaben shugabancin kasar. Sabon shugaban ya zama shugaba farar fata na farko a nahiyar Afirka tun bayan kawo karshen mulkin wariyar lauyin fata a kasar Afirka ta Kudu kimanin shekara 20 da suka wuce.
Shugaban kasar Zambiya Michael Sata ya mutu ne yana da shekara 77 a duniya. Kuma Sakataren Majalisar Ministocin kasar, Dokta Roland Msiska ne ya sanar da mutuwar shugaban kasar shekaranjiya Laraba. Marigayin ya kwashe watanni yana fama da rashin lafiya, kodayake ba a bayyana ciwon da ya yi ajalinsa ba tukuna.
Mutuwar tasa ta zo ne ‘yan kwanaki bayan kasar ta yi bukukuwan cika shekara 50 da samun ‘yancin kai daga Birtaniya.
Kuma ministan tsaron kasar Edgar Lungu ne ya zamo mukaddashin shugaban kasar bayan fitar da Mista Sata kasar waje don jinya.
Marigayin ya fara shiga siyasa ne a shekarar 1980, ya samu shaidar zama gwamnan da ya fi kowane aiki lokacin da yake gwamnan Lusaka, babban birnin kasar. Kafin hakan ya taba yin aikin dan sanda da aikin jirgin kasa da kuma zama memba a kungiyar ’yan kwadagon kasar lokacin mulkin mallaka.
Mista Sata ya samu nasarar zama shugaban kasa ne a shekarar 2011 a karo na hudu yana neman kujerar.