An nada Farfesa Saleh Pakistan Shugaban Majalisar Malaman Kano

Kungiyar na zargin Sheikh Ibrahim Khalil da amfani da ita domin biyan bukatunsa.

An nada Farfesa Saleh Pakistan Shugaban Majalisar Malaman Kano

Majalisar Malaman Kano yayin da take yanke hukunci

Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta nada Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugabanta na riko.

Hakan na zuwa ne bayan da Majalisar ta sauke shugabanta kuma fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil kan zargin ci da addini.

Majalisar ta zargi Sheikh Ibrahim Khalil da siyasantar da zaurenta tare yin amfani da ita don biyan bukatar kashin kai.

Sheikh Ibrahim Khalil

Malaman, wadanda suka hada da wakilan darikun Tijjaniyyah da Kadiriyya da kuma Izala, sun sanar da daukar matakin ne a yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Kano ranar Litinin.

Sheikh Abdullahi Pakistan, shi ne Shugaban kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’ah Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS), reshen Jihar Kano.

Kafin nadin nasa, Farfesa Pakistan dai shi ne Shugaban Izala na Jihar Kano kuma Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar.

Da yake jawabi yayin taron a madadin sauran malaman, Sakataren Majalisar, Imamu Jamilu Abubakar ya ce sun dauki matsayar ne bayan tattaunawa tare da samun dukkan bangarorin addinin Musulunci da ke Jihar.

Ya ce, “Sheik Khalil ya dulmuyar da Majalisar cikin harkokin siyasa sakamakon yadda yake fada da dukkanin gwamnatin da ta zo; ya yi fada da Shekarau, ya yi da Kwankwaso, yanzu kuma yana da yi da Ganduje.

“Dalilin fadan kuma shi ne duk sun hana shi takara, wanda hakan ya haifar da rashin cin moriyar gwamnati ga wannan majalisa, kamar yadda ita ma gwamnati ba ta amfana daga shawarwari na wannan majalisar.

“Kazalika, yana gabatar da tarukan siyasa na kashin kansa a ofishin Majalisar Malamai, sannan kuma Majalisar ba ta da wani takamaiman aiki da take motsi ko kuma samar da fatawa a kan sabbin mas’aloli na zamani da su kan taso.

“Irin wannan majalisa ba ta bukatar dan siyasa mai neman tsayawa takara,” inji Imam Abubakar.

Bugu da kari, malaman na zargin Sheik Khalil da cewa da yawa daga cikin irin fatawoyin da yake bayarwa sun saba da Mazhabar Malikiyya wacce mafiya ’yan Jihar suke bi.

To sai dai yunkurinmu na jin ta bakin Malamin kan matakin ya ci tura sakamakon bai amsa kiran wayar wakilinmu ba ko sakon kar-ta-kwanan da ya tura masa, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Majalisar Malaman dai ita ce Majalisa mafi girma wacce ta hada malamai daga bangarorin addinin Musulunci daban-daban a Jihar.